An Gudanar Da Taron Samar Da Hanyoyin Zaman Lafiya A Kano

0
338

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.


KUNGIYAR mata masu rajin samar da zaman lafiya watau “Women Peace Council” reshen Karamar hukumar Nasarawa, ta gudanar da wani taro na wayar da kai dangane da kyautata zaman lafiya da kaunar juna a Karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano.

Taron wanda aka yi a makarantar yan mata ta Badawa ya sami halartar wakilan kungiyoyin mata dake yankin wadanda suka hada da Badawa, Gwagwarwa, Hotoro, Tudun Wada da kuma Gama bisa jagorancin shugabar majalisar matan Hajiya Zainab Ali Musa.

Haka kuma, an gabatar da jawabai tare da fito da abubuwan dake haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma mazauna unguwa daya ko wasu unguwanni makwabta inda kuma aka tattauna hanyoyin samar da maslaha kafin tashin wata fitina.

A jawabin ta ga mahalarta taron Wanda dukkanin su mata ne, Shugabar majalisar mata masu rajin tabbatar da zaman lafiya, Hajiya Zainab Ali Musa ta yi dogon jawabi kan manufofin wannan kungiya tare da makasudin shigo da ita cikin al’umma a wannan lokaci da ake ciki.

Sannan ta bayyana cewa iyaye mata suna da muhimmiyar rawar takawa wajen kyautata tarbiyyar yaransu tun suna kanana, tare da sanar da cewa yana dakyau iyayen yara musamman mata su kara zage damtse wajen ganin yaransu suna cikin yanayi mai kyau na ilimi da tarbiyya tun daga gida.

Haka kuma ta nunar da cewa lokaci ya yi da iyaye mata zasu kara himma wajen tabbatar da cewa yaransu suna kauracewa dukkanin wasu gurare da ake koyar da rashin tarbiyya da kuma tabbatar da cewa dukkanin abokan da suke mu’amula dasu mutanen kirki ne.

A karshe, Hajiya Zainab Ali Musa ta yi karin haske Kan yadda wannan kungiya za ta ci gaba da shiga kowane lungu da sako domin wayar da Kan al’umma musamman iyaye mata wajen ganin ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a unguwanni da garuruwa ta yadda za a sami karuwar arziki.

Sauran wadanda su ka yi jawabai akwai Hajiya Ai’shatu Badawa da Charity Mathew inda su ka yi alwashin yin aiki da gaske wajen ganin ana samun zaman lafiya tun daga tushe, tare da godewa majalisar mata masu rajin tabbatar da zaman lafiya reshen Karamar hukumar Nasarawa saboda shirya wannan muhimmin taro mai albarka.

Leave a Reply