Connect with us

Labarai

An gano gawar manajan otal a otal ɗinsa

Published

on

An tsinci gawar Manajan Darakta na wani shahararren otal a Ilorin a ɗaya daga cikin ɗakunan otal ɗin nasa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara, CSP Okasanmi Ajayi, ya bayyana haka a Ilorin ranar Juma’a cewa wani mai kula da otal din ya kai rahoton wani da ake zargin kisan kai ga ‘yan sanda a Ilorin ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa, nan take aka aika da tawagar jami’an tsaro zuwa otal ɗin, kuma an tarar da marigayin a kwance babu motsi a kan gadon ɗakin otal ɗin.

Mista Ajayi ya bayyana cewa gawar ba ta nuna alamun tashin hankali ba kuma ya ba da tabbacin cewa ‘yan sanda za su ƙara yin bincike kan musabbabin mutuwar.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar yaro ɗan wata 16 a Bauchi, an cire wasu sassan jikinsa

“Likitoci a wani asibiti sun tabbatar da mutuwar shugaban otal ɗin kuma an ajiye gawar a ɗakin ajiye gawa kafin a gudanar da bincike.

“Za a bayyana cikakken bayanan binciken da wuri-wuri,” in ji Ajayi.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Published

on

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Daga Haruna Abdulrashid

Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kebbi, Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar Mni, ya karrama Shugaban hukumar jin daɗi da walwalar Alhazzai ta ƙasa, Malam Jalal Muhammad Arabi da sarautar (ƊAN BURAN GWANDU BABBA) inda mai martaba sarki ya aike da tawaga zuwa birnin tarayya Abuja domin gabatar da wannan karramawa zuwa ga Malam Jalal Arabi.

Da ya ke jawabi a madadin mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Aminu Ahmad, Sarkin Fadan Gwandu ya bayyana cewa mai martaba sarkin Gwandu ya amince da bayar da wannan karramawa ga Malam Jalal ne a bisa jajircewa da kuma taimako da yake yiwa Alhazzan Najeriya tare da haɗin kai da yake bawa shugabanni a kan abin da ya shafi harkar aikin Hajji mussaman a bana.

Shi ma shugaban hukumar jin daɗin da walwalar Alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji Faruƙu Musa Yaro Enabo, Jagaban Gwandu, ya bayyana jin daɗin shi matuƙa a kan wannan karramawar da aka yi wa maigidan shi.

Ya kuma yabawa mai martaba Sarkin Gwandu Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar akan yadda yake gabatar da kyakkyawan jagoranci zuwa ga Al’ummar Gwandu.

Wannan bayar da takardar karramawa ta sarautar (ƊAN BURAN GWANDU) Sun haɗa da Alh Aminu Ahmed Sarkin Fadan Gwandu, Alh Aminu Abubakar Gulumbe Uban ƙasar Gulumbe, Alh. Mustapha Ka’oje Sarkin Bargun Ka’oje, Alh Lamiru Shehu Sakataren Sarakunan jihar Kebbi, Alh Faruƙu Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu, Alh Usman Osho da Alh Rilwanu Awwal.

Mai girma Shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi, Malam Jalal Arabi, ya bayyana jin daɗin shi sosai ganin wanan karramawa da ya samu daga masarautar Gwandu.

Ya kuma ce jihar Kebbi ta zama gida a gareshi ganin yadda yake samun karramawa da mutuntawa a jihar ya kuma bayyana mana irin mutunci da zumunci dake tsakanin shi da shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi.

Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu ya kuma yi godiya da jinjina zuwa ga Maigirma Gwamnan jihar Kebbi His Excellency Comrd Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu akan irin yadda yayi ɗawainiya ga Alhazzan jihar shi.

Continue Reading

Labarai

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al’umma – Shaikh Bala Lau

Published

on

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al'umma - Shaikh Bala Lau

Mun gana da shugaba Tinubu mun isar masa saƙon al’umma – Shaikh Bala Lau

Daga Idris Umar, Zariya

A ranar Alhamis tawagar malaman Najeriya ta gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu dangane da halin da ƙasa ta ke ciki kan batun zanga-zanga da wasu ke ƙiran a yi dalilin halin matsi da tsadar rayuwa.

Rahoton sun nuna cewa jim kaɗanne bayan kammala ganawar, shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labarai cewa shugaban ƙasa ya karɓi koken da suka je masa da shi.

“Mun faɗa mar halin da al’umma suke ciki na tsadar rayuwa, taɓarɓarewar tsaro da wahalar rayuwa, ya kuma ce dan Allah a ja hankalin al’umma a ba su haƙuri nan gaba kaɗan za a ga sauyi da gyara kan ƙorafe-ƙorafen da ake yi”. In ji Bala Lau.

KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya – ‘Yan Najeriya

Daga nan kuma, Shaikh ɗin ya ja hankalin al’umma da su yi haƙuri su cigaba da addu’a, “ba mu da ƙasar da ta fi Najeriya kar mu rusa ƙasarmu da kanmu”. Inji Shaikh Bala Lau.

Continue Reading

Ilimi

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Published

on

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Daga Idris Umar, Zariya

Kwamishinar kula da ilimin firamare da na Sakandire ne ta bayyana ƙudirin gwamnatin jihar mai ci yanzu na ci gaba da bayar da ƙarin horo ga malamai a faɗin jihar don samar da ƙwararrun malamai da suka iya sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa da za su yi gogayya da takwarorinsu a faɗin duniya.

Hajiya Zainab Musa Musawa ta bayar da tabbacin hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar duba yadda shirin horar da malamai 10,000 da suka haɗa da sabbin ɗauka 7,000 a kan dabarun koyarwa na ƙarni na 20 ke gudana.

Kwamishinar ta kai ziyarar ne a makarantar firamare ta Modoji inda ake gudanar da bayar da horon na yini 3 wanda Ma’aikatar kula da ilimin firamare da na Sakandire, hukumar ilimin bai ɗaya da kuma haɗin gwiwa da shirin bunƙasa ilimi matakin jiha (TESS) suka shirya.

KU KUMA KARANTA: Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

Hajiya Zainab Musa Musawa wanda ta zagaya azuzuwa ta kuma tattauna da masu bayar da horon da Kuma malaman, ta bukace su da suyi amfani da lokacin su fahimci Abunda aka koyamasu don bunkasa tsarin koyo da koyarwa a jihar.

A yayin ziyarar dai Kwamishinar ta samu rakiyar Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Hajiya Mairo Mohamed Othman, Mai baiwa Gwamna shawarma akan ilimi Nura Sale Katsayal sauran Daraktocin Ma’aikatar.

Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa wadda jami’in hudda da jama’a na Ma’aikatar Malam Sani Ɗanjuma Suleiman ya Sanyama hannu a katsina.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like