An fara shiga kotu tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyar ASUU

Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin ministan ƙwadago, Mista Chris Ngige, sun maka ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya wato ASUU ƙara a kotun ɗa’ar ma’aikata.

A wata takardar da ministan ya tura kotun, Ngigen ya bayyana cewa suna so su sa halacci ko rashin halaccin tafiya yajin aikin a shari’ance.

In da za a iya tunawa, ƙungiyar ta ASUU tana yajin aiki ne tun kusan watanni 7 da suka shuɗe a bisa abin da ASUUn ta kira sakacin gwamnati da kuma rashin cika alƙɗawuran da gwamnatin ta ɗauka da kanta na inganta harkokin ilimin jami’a.

Wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa ASUU ta shirya ɗaruruwan manyan lauyoyi masu darajar SAN domin tunkarar lamarin a kotu. Haka ita ma gwamnatin tarayyar ta shirya nata tawagar lauyoyin domin kalubalantar kungiyar.

Bayan zaman kotun da aka fara a yau a Abuja, kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 16 ga wannan watan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *