Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wata manhaja da za ta bai wa ƴan ƙasar damar bibiyar ayyukan da take yi don gani ko tana cika alƙawuran da ta ɗauka.
Ofishin Hadiza Bala Usman, mai bai wa shugaban Najeriya shawara ta musamman kan tsare-tsare ne ya ƙaddamar da manhajar da zummar “fayyace” ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu take yi ba tare da ɓoye-ɓoye ba.
Manhajar “za ta bai wa ƴan ƙasa damar bin diddigi da yin nazari da kuma yin tsokaci kan manufofi da ayyukan gwamnati,” in ji Hadiza Bala.
Ta ƙara da cewa manhajar za ta bai wa mutane damar bin diddigin ayyukan da ministoci suke yi kamar yadda suka yi alƙawari tsakaninsu da shugaban ƙasa.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya na shirin fito da sabon katin ɗan-ƙasa mai haɗe da katin banki
Za a iya sauke manhajar mai suna http://app.cdcu.gov.ng a Google Play Store kuma nan da wata guda za a iya sauke ta a Apple Store, in ji gwamnatin Najeriya.
“Abu mafi muhimmanci shi ne, wannan ne karo na farko da ƴan Najeriya za su samu damar bin diddigin ayyukan dukkan ministoci abin da zai sa ƴan ƙasa su kasance wani ɓangare na masu ruwa da tsaki da ke auna ayyukan da gwamnati take yi,” a cewar gwamnatin ta Najeriya.