Kotu ta bayar da umarni EFCC ta tsare Emefiele

0
91

Wata Babbar Kotu da ke birnin Lagos na Najeriya ta bayar da umarni ga hukumar EFCC ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Rahman Oshodi ne ya bayar da umarnin a zaman kotun na ranar Litinin.

Hukumar EFCC, mai yaƙi da masu yi wa arzikin Nijeriya ta’annati, za ta ci gaba da tsare tsohon gwamnan na CBN zuwa ranar 11 ga watan Afrilu inda kotu za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.

Ana zargin Godwin Emefiele da laifuka 26 ciki har da almundahana da halatta kuɗaɗen haramun.

EFCC ta zargi Emefiele da ajiye kuɗin da ya kusa dala biliyan biyu ba tare da bin doka ba.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta gano tare da miƙa wa ƴan fansho na jihar Kano gidaje 324

Kazalika Alƙalin Kotun, ya bayar da umarni a kai Henry Omoile, wanda ake zargi da haɗa baki da Emefiele wurin tafka almundahana, gidan kurkukun Ikoyi da ke Lagos, shi ma zuwa ranar Alhamis don sauraren ƙorafinsa kan bayar da shi beli.

Tsohon gwamnan na CBN yan fuskantar irin waɗannan tuhume-tuhumea wata kotun da ke Abuja.

A watan Yulin 2023 shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga aiki sannan aka ƙaddamar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here