Amurka Ta Gargadi Amurkawa Kan Bulaguro Zuwa Najeriya

0
344

Daga Wakilinmu

Yayin da ake samun karuwar satar mutane da sauran laifuka a Najeriya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tana kira ga Amurkawa da ‘yan kasa biyu da sauran su da su “sake yin shawarar balaguro” zuwa kasar da ke yammacin Afirka.

Shawarwarin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan masu tafiye-tafiye, wanda aka fitar a ranar 4 ga watan Janairun nan, ya yi gargadin cewa “laifuka na tashin hankali – kamar fashi da makami da kai hare-hare da satar motoci da garkuwa da kuma fyade – ya zama ruwan dare a duk fadin kasar.

Satar mutane don neman kudin fansa na faruwa akai-akai, galibi ana kai hari ga ’yan kasa biyu da suka koma Najeriya ziyara, da kuma ‘yan kasar Amurka da ake da masaniyar suna da arziki.

A wannan nan ranar ne kuma, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana masu dauke da makamai a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito. Ayyanawar ta ba da karin takunkumi da hukunci ga masu laifi da wadanda suka taimaka aka aikata laifin.

Shawarar da Amurka ta bayar ta hada da gargadin “kada ayi tafiya” zuwa jihohin Borno da Yobe da kuma arewacin Adamawa saboda ta’addanci da matsalar garkuwa da mutane, da kuma irin wannan gargadi ga jihohin Bauchi da Gombe da Kaduna da KanodaKatsina da Zamfara saboda sace-sacen mutane.

Yankunan bakin teku kamar jihohin Akwa Ibom da Bayelsa da Kuros Riba da Delta da Ribas – ban da Fatakwal – su ma suna duk cikin jerin “kada ku yi tafiya”.

Kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka ta fuskanci matsalar rashin tsaro, ciki har da yawaitar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa. A jihar Kaduna kadai, gwamnati ta ce an yi garkuwa da mutane 1,723 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2021, idan aka kwatanta da kusan 2,000 a duk shekarar da ta gabata.

Leave a Reply