Connect with us

Kiwon Lafiya

Amfanin goruba a jikin Ɗan adam

Published

on

Daga Fatima MONJA, Abuja

Ana kiran wannan itaciya da goruba a harshen Hausa, da turanci kuma ana kiranta da ‘Doum palm tree’ yayin da suke kiran ‘ya’yanta da ‘Doum palm Fruits’. Itaciya ce mai tsohon tarihi da al’ummai daban-daban na duniya suka jima su na amfani da ita wajen samar da magungunan cutuka ma su yawa.

KU KUMA KARANTA:Amfanin kokumba a jikin ɗan Adam

Misali masana sun ce tun fiye da shekaru 2000 ƙasar Sin ke amfani da ita don warkar da cutukan dake addabar bil adama.

Hakanan, mai karatu na sane da tsohon tarihin ƙasar Misra, wacce ita ma masanan su ka bayya cewa shekaru aru-aru da suka shuda suke amfani da goruba don samar da magani.

Kodayake, mu na cikin ƙarni da ake bugun ƙirji da ci gaban zamani, saboda ƙirkire-ƙirkire, da nazarce-nazarcen kimiyya, amma duk da haka masana a wannan zamani sun gano irin rawar da goruba za ta iya takawa wajen samar da waraka ga wadansu cutukan dake addabar dan-adam.

Kafin mu fara bayyana irin amfani da ta ke da shi ga lafiyarmu, ga jerin sanadaran da binciken wannan zamani ya tabbatar goruba na ƙunshe da su. Sanadaran su ne: Bitamin A, B da na C, sai sanadarin ‘Zinc’ da ‘Calcium, Kalium, Iron, Fibre, Protein, Glucose, Nitrogen, da kuma phosporos.

Bayan nazari mai zurfi da mujalla ta gudanar, ta samu nasarar ganowa tare da jero amfanin goruba ga jikin dan-adam kamar haka:

1 Maganin Cushewar Ciki.

Kamar yadda mai karatu ya sani ɗaya daga cikin hanyoyin da masana a fannin lafiya ke bayarwa domin mangance cushewar ciki ita ce, yawaita cin ‘ya’yan itatuwa, musamman waɗanda ke ƙunshe da wani sanadari na Fibre. Saboda haka, ɗaya daga cikin ‘ya’yan itatuwa da za ku iya ci mai ɗauke da wannan sanadarin mai yawa ita ce’ ya’yan itacen Goruba. Allah Ya yiwa goruba baiwar wannan sanadari mai yawa Kamar yadda aka ambata a sama, saboda haka ne take da matuƙar fa’ida wajen warware wannan matsala.

  1. 2. Magance Zafin Jiki

Yanayin zafi wani irin yanayi ne dake haifar wa mutum kasala da kuma zafin jiki, musamman a Ƙasashe ma su zafi irin namu. Saboda haka, idan kuna neman wani abu da zai iya sanyaya  jikinku sannan ku samu kuzari a lokacin zafi, to ‘ya’yan goruba su ne mafita. A irin wannan yanayi da ɗan-adam ke da buƙatar sanyaya jiki da kuma samun kuzari, ba’a buƙatar haɗa ta da wani abu,  za’a ci gorubar ne zallanta.

  1. Rage Yanayin Damuwa

Sau da yawa mukan fuskanci matsalolin da zasu iya haifar ma na da damuwa da ake kira ‘stress’ da turanci, sakamakon al’amuran da muke gudanarwa yau da kullum. To, idan mutum ya tsinci kai a irin wannan yanayi lokaci ne da zai nemi goruba, musamman wacce aka tace ta aka yi lemonta ko shayinta.  Masana sun tabbatar da cewa shan ruwan goruba na iya kwantar da hankali cikin sauki.

Tuni nazari da masana suka gudanar ya tabbatar da cewa sanadarin bitamin C na taimakawa wajen rage matsalolin damuwa irin wadda mu ka ambata a sama. Wannan ya sa yawan wannan sanadari na bitamin C  da goruba ke kunshe da shi  ke taka muhimmiyar rawa wajen magance wannan matsala. Wani bincike da aka gudanar  ya nuna cewa bai wa marasa lafiya dake fama da matsalar damuwa sanadarin bitamin C  na matukar taimakawa wajen inganta yanayinsu.

4.  Inganta Lafiyar Ƙoda

Ko mai karatu ya san amfanin ƙoda a jikinsa ? Ƙoda na ɗaya daga cikin muhimman sassan jikinmu.  Saboda Ƙoda ce ke da alhakin tacewa tare da fitar da duk wani sanadari da ka iya cutar da jikinmu.  Wannan dattin jiki da ƙoda ke tacewa na fita ne ta hanyar fitsari. Akwai wani sanadari mai suna  ‘Phosphoros’ a turance dake da yawa cikin ‘ya’yan itaciyar goruba da ke taimakawa wajen inganta lafiyar ƙoda.

5.  Magance Ƙurajen Fata.

Ƙaikaiyi, raɗaɗi da damuwa ba su kaɗai ne illolin ƙurajen fata ba, a’a baya ga haka su kan yi lahani ga fatar jikinmu ƙwarai da gaske. To amma ‘ya’yan goruba na iya taimakawa wajen magance irin wannan matsala ta fata. Ko da yake har zuwa wannan lokaci babu wani nazari game da hakan. Amma, wasu daga cikin masana, sun yi amannar cewa ‘ya’yan goruba na iya warkar da cututtukan dake shafar fatar dan-adam.

6.  Samar Da Kuzari Ga Jiki.

Mu na bukatar kuzari domin samun damar aiwatar da ayyukanmu na yau da kullum cikin kuzari.

7.  Gyaran Gashi.

Hakanan dai akwai nazari da aka gudanar wanda ke tabbatar da yadda wannan ‘yar itaciya ke taimakawa wajen tsirar gashi ga dan-adam. Yadda za a yi domin samun wannan fa’ida shi ne, za a jiƙa ta, sannan ake wanke gashin da wannan ruwan, da sannu za a ga biyan buƙata.

8. Ƙarfin Haƙori Da Ƙashi.

Ba shakka yawan cin goruba na ƙara ƙarfin ƙashi da na hakori. Ba don komai ba sai don an tabbatar da ta na kunshe da sanadarin ‘Calcium’ wanda ke da matukar muhimmanci wajen ginin kashi da karfinsa.

9.  Maganin Hawan Jini.

Kamar yadda aka jero sanadaran da wannan ‘yar itaciya ta ƙunsa, haka wani nazari ya nuna tana taimakawa ma su fama da matsalar hawan jini. Sai dai a nan an bada shawarar samun garinta, sannan a jika shi, bayan an tabbatar da ya jiƙa sai a sha aƙalla sau uku a rana.

10.  Maganin Basir.

Ga duk ma su fama da wannan matsala ta basir, mu na yi mu su albishir da yin amfani da goruba don samun sauki daga wannan matsala. Domin magance matsalar basir za’a yawaita cin ta ne ba tare da hada ta da komai ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta hana amfani da sirinjin allura na ƙasashen waje a manyan asibitoci ƙasar

Published

on

Gwamnatin tarayya ta umurci dukkan shugabannin manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su sayi allura da su riƙa amfani da allura da da ake ƙera su a gida kuma hukumar NAFDAC ta amince da su.

Sabuwar umarnin na ƙunshe ne a cikin wata takardar ga dukkan shugabannin asibitoci mai ɗauke da sa hannun ƙaramin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa, a yau Juma’a.

Ministan ya ce an ba da wannan umarnin ne domin bunƙasa samar da kayayyakin da ake ƙera wa a cikin gida da kuma kare masana’antun ƙasar daga kwararar kayayyakin ƙasashen waje.

Sanarwar ta kuma umarci hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka ƙera daga ƙasashen waje.

Alausa ya ce ɓangaren lafiya ya gano masana’antar har haɗa magunguna ta cikin gida da ke samar da allura da sirinji waɗanda ke cikin matsala matuƙa saboda wannan mummunar harkar.

Ya kuma ce daga cikin kamfanonin har haɗa magunguna guda tara na cikin gida da suke samar da allura da sirinji shekaru takwas da suka gabata, shida sun rufe saboda zubar da kayayyakin da ba su da inganci a kasuwa.

KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

“Shugaban ƙasa ya ba da umarnin cewa dole ne a daina wannan. Dukkanmu mun amince da ɗaukar matakan da suka dace don magance wannan mummunan yanayi cikin gaggawa.

“A bisa haka, hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka ƙera daga ƙasashen waje.

“Haka kuma shi ne a soke jerin sunayen kamfanonin da ke da hannu wajen shigo da waɗannan kayayyakin da ke ci gaba,” in ji shi

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Amfanin ‘Dental floss’ a haƙora don tsaftace baki

Published

on

Daga Aisha Musa Auyo

Dental floss dai wani zare ne siriri na roba da ake sawa a tsakanin haƙora don cire abincin da ya maƙale a wurin. Wannan abinci da ke maƙale a tsakanin haƙora, brush ba ya fitar da shi. Shi ne yake taruwa ya zama ‘plaque’. Shi plaque ɗin wannan abincin da ya maƙale ne yake taruwa sai ya zama abincin bacteria.

Wannan dattin yana sa baki wari, yana sa haƙora su canza kala. Yana sa haƙora su yi ta ciwo wataran ma har sai an cire haƙorin, domin wannan bacteriar da ke ci daga gareshi tana kashe haƙori.

To shi wannan zaren yana zuwa a nau’i daban-daban, an yi shi ne siriri yadda ze iya shiga tsakanin haƙora yana fito da duk abin da ya maƙale ba tare da an wahala ba ko an ji zafi. Wani yakan zo da ƙamshin minti, vanilla, da sauransu, wani kuma kawai zaren ne babu ƙamshi.

Mafi yawancin ciwon haƙori ko warin baki wannan maƙallen abincin ke kawo shi. Idan mutum ya je Asibitin haƙori, akan yi masa wannan sakace tsakanin duk haƙoransa duka. Wato duk ranar da kuka fara flossing zai sha mamakin abin da zai fito tsakanin haƙoranku.

KU KUMA KARANTA: Sama da mutane miliyan 73 ne ke fama cutar ruɓewar haƙora a Filipin

Wato abin ya bani mamaki da na tambayi mutane ko suna flossing na ga da yawansu ba su ma san mene ne shi ba. Kamata ya yi flossing ya zama normal kamar brush. A ƙa’ida akan so mutum ya yi wannan sakacen tsakanin haƙoran kamar sau biyu a rana, yadda yake brush, amma mutum zai iya yin fiye da haka. In da hali duk lokacin da mutum ya ci abinci ya kamata ya yi flossing.

Akwai mouth wash da kan taimaka wajen fitar da waɗannan maƙallalun abincin, yayin da aka kurkure baki da shi na mintuna. Haka zalika, kurkure baki da ruwan kananfari ma na taimakawa wajen fiddasu. Amma babu abin da ya kai saka wannan zare a tsakanin haƙora ɗaya bayan ɗaya fitar da wannan abu da ke maƙalewa a tsakanin haƙoran.

Dan Allah a guji tsinken sakace, ba ɗaya yake da floss ba. Shi tsinken yana da kauri yana sa a samu rami tsakanin haƙoran da ake yawan sakace wa. Sannan katako ne yakan karye ma, kuma yakan jima mutum rauni.

A taƙaice, yin floss na ƙara wa mutum lafiyar haƙora, kyan haƙora, numfashi mai tsafta, da kuma jin daɗi wajen mua’amala da jamaa. Yin floss na raba mutum da ciwon haƙori, da kuma dauɗar haƙora. Floss na da sauƙin kuɗi sosai, ana iya samunsa a manyan shaguna, ko asbitin haƙori, har ma da wurin masu sayar da robobin abincin biki, domin ana sa shi a cikin packs ɗin abinci.

Dan Allah ka da mu yi wasa da yin floss. Akwai Hadisin da Annabi Muhammad (SAW) ya ce, ba dan ka da ya takurawa al’ummarsa ba, da ya mayar da yin aswaki kafin yin kowacce sallah ya zama wajibi. Wannan yana nuna mana tsantsar amfanin tsaftar baki ko a addini ma.

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 a Yobe

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Yobe ta ce cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.

Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.

Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.

KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta musanta mutuwar mutum 200 sanadiyar baƙuwar cuta a Yobe

Dakta Gana ya kuma ce an tura jami’an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Potiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma’aikatar take na daƙile cutar.

Ya ce ma’aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.

Yankunan arewacin Najeriya na fama da matsanancin zafi a tsukin nan, yanayin da ke haddasa cutar ta sanƙarau.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like