Amfanin Bagaruwa 10 a jikin ɗan Adam

0
94

Binciken masana ya tabbatar da cewar itacen bagaruwa na da matukar amfani sosai tun jikin ɗan Adam kama daga ganye, itace da kuma ‘ya’yanta.

Noman itacen Bagaruwa ya fi yawa a busassun wuraren sannan ƙasar Australia da ƙasashen Larabawa na cikin kasashen da suka fi nomanta.

Ga amfanin da yake yi a jikin mutum:

  1. Bagaruwa na maganin tsutsar ciki.
  2. Itacen bagaruwa na maganin gudawa mai tsanani.
  3. Yana kuma kawar da matsalar zubar jini.
  4. Bagaruwa na maganin ciwon hakori: Ana daka ‘ya’yan Bagaruwa a riga zubawa ko kuma a samu ‘ya ‘yan ta wayanda basu bushe ba a riqa matsa ruwanta a cikin wurin.
  5. Bagaruwa na maganin ciwon sikari wato ‘Diabetes’.
  6. Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki.
  7. Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata.
  8. A samu ganyen Bagaruwa a tafasa idan ya tafasu a juye a buta a riga wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido.
  9. Yana kara karfin mazakuta.
  10. Bagaruwa na maganin cutar Hepatitis C.

Leave a Reply