Amfani 7 na manja ga jikin ɗan Adam

0
436

Babu shakka bishiyar kwakwar manja na ɗaya daga cikin bishiyoyi a duniya masu cike da albarkatu kuma daga cikin waxannan albarkatun ne akwai mai wanda ke da launin ja.

Ana cire man jar ne daga kwakwar man da bishiyar ke fitarwa.

Kwakwar na da launin duhu kuma ana iya ganeta daga kamshinta na daban da kuma ɗanɗanonta,kamar yadda aka sani, tana da amfani ga lafiya kuma ana amfani da ita a yankunan kudanci da gabashin Najeriya.

Kwakwan manja, wasu na ce mishi ƙwara

Tana maganin manyan cutuka masu matuƙar barazana ga lafiyar ɗan Adam, kuma ana iya amfani da manjan wurin girki don kuwa bata da sinadarin cholesterol.

Likitoci na shawartar masu fama da cutukan zuciya da su kiyaye duk wani mai da ke kunshe da sinadarin cholesterol, hakan yasa suke shawartar a dinga amfani da manja wurin girki.

Kamar yadda bincike ya nuna na zamani, manja na ƙunshe da sinadarin Fatty Triglycerides kuma ana iya samun sa a cikin ababen amfani masu yawa.

Ga 7 daga cikin manyan amfanin manja ga jikin ɗan Adam.

1.Ana amfani da man wurin maganin farfaɗiya,a gargajiyance, ana amfani da manja wurin maganin shiɗewa ga kananan yara, wannan kuwa yana taka rawar gani wurin yakar cutar farfadiya.

2.Manja na ɓoye shekaru ga mai amfani da shi, sakamakon kunsar sinadarin Vitamin E da A da ke cikin manja, kuma man na kashe wasu alamun tsufa da za su iya nuna wa a jiki.

KU KUMA KARANTA:Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai

3.Manja na sa tsayin gashin kai, yana kuma bada matukar mamaki a ɓangaren tsayin gashi, yana sa cikar gashi tare da hana zubewarsa, yana kuma ƙara ƙarfin gashi tare da walkiyarsa.

4.Manja na taimakawa wurin fitar da miyagun ƙwayoyin cuta daga jiki, ba wai ƙwayoyin cuta kaɗai ba, manja na tsarkake kwayoyin halitta tare da inganta su a jikin ɗan Adam.

5.Manja na tausasa fata, yana tausasa fatar jikin ɗan Adam inda take cire maikon jikinsa, hakan ce ta sa ake amfani da shi wurin yin sabulai da mayuka,haka zalika manja na cire kaikayin jikin

6.Manja na daidaita karfin jini. Sabon bincike ya nuna cewa manja na inganta yawon jiki a sassan jikin ɗan Adam. Hakan yasa yake daidaita jini tare da kariya daga cutar hawan jini.

7.Manja na maganin warin jiki. Sakamakon kamshinsa mai karfi, yana kuma maganin warin jiki idan ana shafawa akai- akai a jiki.

Leave a Reply