Al’ummar Jigawa da ambaliya ta ɗaiɗaita na kokawa kan halin da suke ciki

1
875

Ɗaruruwan mutanen da suka gudu daga garuruwansu zuwa wasu yankuna masu aminci sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya sun koka a kan mawuyacin halin rayuwar da suke ciki.

Hukumomi dai sun tsugunar da mutanen na wucin gadi a makarantun gwamnati, inda a kan ba su taimako, yayin da akasarin su ke zaune a gidajen ƴan uwa da abokan arziki.

BBC Hausa ta ziyarci wani sansani a Haɗejia domin ganin halin da suke ciki. Wata mata da wakilin ya tattauna da ita ta ce, suna fuskantar ƙalubale duk da cewa suna ci suna sha sai dai ta ce “da ƴaƴanmu muna layi ana kallonmu, idan mu manya ne akwai mu da ƴaƴa mata, yaran nan muna taka tsan-tsan da su.”

Ita ma wata mata da ke samun mafaka a sansanin ta ce suna fuskantar ƙalubale ta fuskar kula da lafiya amma ana ta ɓangaren ta ce ba kullum abinci ke wadatar da su ba.

“Akwai sauro a wannan wajen don idan ba ka shiga gidan sauro ba, duk shi ne yake haddasa mana zazzaɓi zazzaɓin nan na yara domin ƙalau muka zo”. in ji ta.

Alhaji Abdulkadir Umar Bala TO, Shugaban ƙaramar hukumar Hadeja ya ce suna iya ƙoƙarinsu wajen tallafa wa mutanen. “Gwamnati tana ba da tallafi na ɗauki sannan al’umma da ƙungiyoyi da ƴan siyasa, kowa yana kawo gudummawarsa domin tallafa wa mutanen nan.

“Sannan mu kuma muna kai musu magani, abin shimfiɗa da atamfofi da duk abin da ya kamata a tallafa”.

Ya kuma musanta iƙirarin wasu da ke cewa abincin da ake ba su ba ya isarsu inda ya ce “duk zance suke, mutum ne idan daɗi ya yi masa yawakomai ma zai iya faɗa,” in ji Alhaji Abdulƙadir.

1 COMMENT

Leave a Reply