Abin da yasa ban yada Atiku akan tayin Naira miliyan 150 ba – Sarkin waƙa

0
417

Fitaccen mawaƙi kana jarumin fina-finan Kannywood, Naziru Ahmad da aka fi sani da Sarkin Waƙa, ya yi ikirarin cewa an yi masa tayin Naira miliyan 150 da kuma mota ta Naira miliyan 80 domin ya jefar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, gabanin zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Sarkin waƙa yana ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa da suka yi waƙoƙin yaƙin neman zaɓen Atiku kuma ya yi tarukan gangamin sa a faɗin Arewa.

Ya yi shahararriyar wakar adawa ta APC mai taken ‘APC Sai Mun Bata Wuta…’

Da yake magana a wani shiri na Sashen Hausa na DW, mawaƙin na Kannywood ya ce ya ƙi amincewa da tayin watsi da Atiku ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Tauraron na Kannywood ya ce yana da yaƙinin cewa Atiku ya fi Tinubu ƙoshin lafiya kuma zai iya taka rawar gani idan ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

KU KUMA KARANTA:Kuyi min addu’a aurena na 6 na ƙoƙarin rugujewa-Adam A. Zango

“Na fifita bukatun kasa fiye da bukatun kaina, an bukaci in bar Atiku ga wani ɗan takara kuma a biya ni kuɗi Naira miliyan 150 da kuma wata mota da ta kai Naira miliyan 80 amma na ki.

“Na yi watsi da tayin ne saboda na san Atiku zai samar da shugabanci nagari tare da ceto Najeriya daga halin da take ciki a halin yanzu.

“Ta yaya zan goyi bayan Tinubu wanda ba shi da lafiya ? Addininmu ya kuma yi mana gargaɗi da cewa mu zaɓi masu lafiya a matsayin shugabanni domin yana ɗaya daga cikin halayen shugaba nagari.”

Leave a Reply