‘Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe ‘yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana mutumin a matsayin Kabir Sani mazaunin unguwar rukunin gidajen ‘Shagari Low-Cost’.
‘Yansandan sun ce maƙwabtan Kabir sun tabbatar da cewar tun daren Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis Kabir ke lakaɗawa ‘yarsa Ummulkhairi duka a kan sai ta amince da zaɓin da ya mata amma taƙi.
Ku kuma karanta: Kotu a Kano ta yanke wa Amarya hukuncin kisa kan kashe Angonta bayan kwana 9 da aure
Rahotanni sun ce abokan ta ne su ka tarar da gawar ta da safe lokacin da suka biya mata su tafi makaranta, abinda ya suka shaidawa ƴan sanda.


