Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

HomeKisan KaiKotu a Kano...

Kotu a Kano ta yanke wa Amarya hukuncin kisa kan kashe Angonta bayan kwana 9 da aure

Kotu a Kano ta yanke wa Amarya hukuncin kisa kan kashe Angonta bayan kwana 9 da aure

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke wa Saudat Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an same ta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwanaki tara kacal da ɗaura aurensu.

A lokcin yanke hukuncin, Mai Shari’a Maryam Sabo ta bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjoji da shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatar. Ta ce lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soran Ɗinki, ya gabatar da gamsassun hujjoji tare da shaidu biyu da suka tabbatar da aikata laifin, lamarin da ya sa kotun ta same ta da laifin kisan kai tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayan kammala shari’ar, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soran Ɗinki, ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin da kotun ta yanke, yana mai cewa an yi adalci bisa hujjojin da aka gabatar.

Sai dai lauyan da ke kare Saudat Idris ya bayyana cewa ba su gamsu da hukuncin ba, yana mai cewa za su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara domin neman a sake duba hukuncin da aka yanke.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

‘Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe ‘yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata

'Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe 'yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata Rundunar 'yan sandan ta bayyana mutumin a matsayin Kabir Sani mazaunin unguwar rukunin gidajen 'Shagari Low-Cost'. 'Yansandan sun ce maƙwabtan Kabir...

‘Yan bindiga sun sace alƙalin babbar kotun jihar Kebbi

'Yan bindiga sun sace alƙalin babbar kotun jihar Kebbi Rahotanni daga jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, 'yan bindiga sun sun yi garkuwa alƙalin babbar kotun jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruƙu Hassan Bunza. Wani mazaunin jihar Kebbi,...

An yi jana’izar mataimakiyar shugabar Mata ta Jam’iyyar APC, Hajiya Mairiga

An yi jana'izar mataimakiyar shugabar Mata ta Jam'iyyar APC, Hajiya Mairiga Jihar Yobe ta shiga cikin makoki bayan rasuwar Hajiya Fatima Mairiga, fitacciyar mataimakiyar shugabar mata ta jam'iyyar APC kuma 'yar siyasa mai daraja da kima, wacce ta rasu a...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.