Hukumar da ke nazarin sauyin yanayi da yadda yake tasiri kan muhallin ɗan Adam ta ƙasa da ƙasa ta bayyana fargaba, game da yadda barazanar tsananin zafi ke tunkarar ƙasashen da ke yammacin nahiyar Afrika.
A wani rahoto da hukumar ta fitar ta kuma ba da shawara ga ƙasashen da ke yankin Sahel cewa su fitar da shirye-shiryen da suka kamata tare da yin gargadi ga al’ummunsu game da tsananin zafin dake tunkarar su domin ɗaukar matakan kan da garki.
A cewar rahoton tun a ƙarshen watan Maris da kuma farkon watan Afrilu, an shaida yadda aka rinka fuskantar tsananin zafi cikin dare ko da rana sama da 40 na ma’aunin Celsius.
KU KUMA KARANTA: Za a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin Najeriya – Nimet
Yanayin matsanancin zafin yafi kamari a ƙasashen Mali da Burkina Faso, in ji rahoton hukumar.
Domin a cewar rahoton Hukumar ta World Weather Attribution sama da shekaru 200 ba’a fuskanci makamancin wannan yanayi na zafi ba a sassan duniya.
Tsananin zafin ranar da ake samu a baya-bayan nan shi ne ya ja hankalin tawagar masana kimiyyar yanayi na Hukumar ta WWA gudanar da wannan bincike cikin gaggawa.