’Yan bindiga sun sace mata biyu ’yan gida ɗaya a Abuja

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun sace wasu ’yan mata biyu ’yan gida yayin wani hari da suka kai kauyen Guite da ke gundumar Chikakore ta ƙaramar hukumar Kubwa da ke Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar bayan sace ’yan mata masu shekaru 14 da 16 sun tsere cikin wani jeji wanda ya yi iyaka da ƙauyen da wasu ƙauyuka maƙwabta.

Bayan kwashe ‘yan matan ne kuma ‘yan bindigar suka ranta a na kare inda suka shiga daji wanda ya haɗa ƙauyen da wasu ƙauyukan masu maƙwabtaka.

Wani mazaunin ƙauyen wanda a buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata.

A cewar majiyar, “’yan bindigar sun kutsa gidan ne ba tare da harbi irin na kan-mai-uwa-da-wabi ba kamar yadda suka saba sannan suka kama ’yan matan guda biyu.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sanye da hijabi sun afka wa ofishin ‘yan sanda a Katsina

Sai dai an yi rashin sa’a a ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja SP Adeh Josephine sakamakon rashin amsa ƙiran wayar da aka yi mata.

Wannan ne dai karo na biyu a ƙasa da wata guda da ’yan bindiga ke yin garkuwa da ’yan mata ’yan uwan juna a babban birnin na tarayya.

Neptune Prime Hausa ta ruwaito yadda a makonnin da suka gabata wasu ‘yan bindiga suka sace mutane daga rukunin gidaje na Sagwari da ke unguwar Dutsen-Alhaji a Karamar Hukumar Bwari da ke Abuja.

Masu garkuwa da mutanen sun kashe huɗu daga cikinsu, ciki har da wata ɗalibar jami’ar Ahmadu Bello, Nabeeha Al-Kadriyar, da kuma Folashade Ariyo mai shekara 13.

An sace Nabeeha ce tare da ’yan uwanta mata biyar da mahaifainsu daga gidansu da ke unguwar Zuma 1 a wajen garin Bwari a ranar 2 ga watan Janairu.

Matsalar tsaro dai na ƙara ta’azzara a birnin na Abuja, lamarin da ke ƙara jefa fargaba a zukatan mazauna birnin.

To sai dai a baya rundunar ’yan sandan birnin ta sha cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin su daƙile matsalar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *