Connect with us

Labarai

Abin da ya sa muka ce za mu rufe kasuwar Potiskum, kuma mu yi zanga-zangar lumana – Shugaban ‘yan kasuwar Potiskum

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

A makon da ya gabata ne, shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan kasuwar Potiskum, Alhaji Nasiru Mato ya fitar da sanarwar cewa za su rufe kasuwannin da suke cikin garin Potiskum, sannan za su gudanar da zanga-zangar lumana. A wannan tattaunawar, Alhaji Nasiru Mato ya bayyana dalilansu na fitar da wannan sanarwa da kuma sauran batutuwa da dama da suka shafi kasuwa da ‘yan kasuwar Potiskum.

Ga yadda hirar ta su ta kasance da wakilinmu Ibraheem El-Tafseer;

NEPTUNE HAUSA: Da farko muna so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

ALHAJI NASIRU MATO: Suna na Alhaji Nasiru Mato shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan kasuwar Potiskum da kewaye.

NEPTUNE HAUSA: Ko mene ne ya faru aka ga shafinku na na ‘yan kasuwar Potiskum (UMAPO) kun fitar da sanarwar za ku fita zanga-zangar lumana, sannan za’a rufe kasuwannin cikin garin Potiskum?

ALHAJI NASIRU MATO: Eh to! Abin da ya sa muka fitar da sanarwar za mu fita mu yi zanga-zanga na lumana, to ba komai ba ne ya sa, sai abin da ya ke faruwa tsakaninmu da ƙaramar hukumar Potiskum. To mu dai mun sani cewa akwai gwamnati na ƙaramar hukuma da jiha da na tarayya duka. Kuma mun san ko’ina akwai shugaba da ya ke shugabantar wannan wuri. Sannan muma a matsayinmu na shugabanni wanda mu ke wakiltar al’umma, kuma ɓangarenmu shi ne ɓangare ma fi rinjaye, ɓangare ma fi al’umma.

Ba ma a Potiskum ba, a ko’ina, duk duniya ma ɓangaren ‘yan kasuwa ya fi kowane ɓangare yawan al’umma. Ba wai mun ce kowane abu ne sai an sanar da mu idan za’a yi ba, amma akwai abin da idan ya shafeku, yana da kyau kafin a yi, a tuntuɓe ku, a ji shawararku. Duba da yanayi da ake ciki, na matsatsi da rashin abin yi. Har Allah ya sa ana iya samun wasu suna iya yin sana’a su da kansu, domin su ciyar da iyalansu, su taimaki wasu mutane, ba su ɗora wa gwamnati nauyi ba. Ba su roƙi kowa ba, ba su zama ‘yan ta’adda ba.

To muna ganin wannan babban abin alfahari ne, ga duk inda shugaba ya ke, idan har ya kasance yana jagorantar irin waɗannan mutane a ƙaramar hukumarsa ko a jiharsa. Zai iya yin alfahari da bugar ƙirji.

To sai muka samu labarin gefen ‘Police Station’ an ba su takarda su ta shi, saboda wani dalili. Sannan sai ofishin ‘Road Safety’ an ba su sati biyu su kwashe kayansu, ana so su tashi, saboda gwamnati za ta gina ‘Plaza’ domin a sayar wa mutane. Ka ga a nan akwai ayar tambaya, gwamnati za ta yi plaza. To plaza ɗin da za ta yi, ita gwamnati ɗin ne za ta zuba kaya a ciki ta dinga sayar wa mutane? Ko kuma ‘yan kasuwar da take kora su bar wajen, take faɗa da su, sune take tsammanin za su saya a su yi kasuwanci a ciki.

Akwai ayar tambaya. Misali ni ne nake so na yi abu na ci gaba don kai, sai nake faɗa da kai ina korarka, to idan na yi abin ni ne zan sake kiranka mu yi sulhu, ka zo ka yi amfani da abin?

Sai na uku, akwai kasuwar NPN. Wadda tana da shekara 34 da yin waɗannan shagunan ‘shopping complex’ ɗin, wanda Alhaji Barde Gadaka ya yi, wanda kuma an bawa ‘yan siyasa manya da ƙanana a wancan lokacin, kuma gwamnatin wancan lokacin ita ta bayar.

Ai gwamnati ba ta fi gwamnati ba, mu abin da muka ɗauka a gwamnati kawai ci gaba ne, idan ka zo za ka ɗora a inda wani ya tsaya ne. ba wai idan ka zo ka ce wane bai iya ba, wancan bai iya ba, kai ne ka fi kowa iyawa. Ƙaramar hukuma ta ce, ya ce ya soke takardar izini na mallakar wannan wuri da aka bawa mutane.
Kenan waccar gwamnatin da ta bayar a baya, ita ba ta iya ba kenan? Sai yace shi ba ruwansa da wadda gwamnatin ta bayar a baya. Shi da wanda yake cikin shago yake Magana a yanzu. Ka ga wannan wata rigima ce wadda za a kunno ta, kuma ba a san ƙarshenta ba. Saboda waɗanda aka bawa shagunan a baya, ‘yan siyasa ne, kuma an basu ne don su ma su samu na cefane a gidajensu.

Ba mu ce gwamnati shagunan nan ba nata bane fa, ba mu ce gwamnati kar ta sabunta takardun shagunan ba fa, amma sai a bi bisa tsari. Ba inda ba a sayar da ‘allocation’ ko na gida ko na kasuwa, ba inda ba a sayar dashi. Idan ma laifi ne, to duk ƙasar nan ana yi, a kowace jiha da ko’ina.

A jihar Yobe muna da ƙananan hukumomi 17, a dukkan waɗannan ƙananan hukumomi babu inda ake irin wannan abun sai a Potiskum kaɗai. A Potiskum kaɗai ake ƙirƙirar irin waɗannan abubuwa.

To wannan shi ne dalilinmu, muka ga cewar tun da ba a neman mu, ba a san damu ba, kuma muma ‘yan jam’iya ne. Kuma mune muka cewa mutanenmu a zaɓi jam’iyar gwamnati, domin samun zaman lafiya. Ba mu zaɓi gwamnati don a ci mutuncinmu ba ne. To wannan shi ne dalilinmu na shirya gudanar da zanga-zangar lumana.

NEPTUNE HAUSA: To kwatsam, sai muka ga sanarwar cewa an janye wannan zanga-zangar lumana da aka shirya, ko me ya faru aka janye gudanar da ita zanga-zangar?

ALHAJI NASIRU MATO: To kasan an ce wai gaba da gabanta. To daga gwamnatin jihar Yobe, aka turo mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro. Aka ƙira mu da jami’an tsaro da wakilan sarakuna da shi shugaban ƙaramar hukumar ɗin da muƙarrabansa. Muka tattauna, daga ƙarshe dai muka cimma matsaya cewa, mu, mu yi haƙuri, kar mu yi wannan zanga-zanga da muka shirya. Su ma ƙaramar hukuma su dakata da ƙudurinsu na abin da suke niyyar yi, har sai mun zo mun zauna a teburi, an warware inda matsalar take. To wannan shi ne ya sa muka janye.

NEPTUNE HAUSA: To ku yaya kuke so tsarin tafiyar da shagunan ya kasance a kasuwannin Potiskum, idan aka bawa mutum ‘allocation’?

ALHAJI NASIRU MATO: Ka ga kamar mu abin da muka sani shi ne, mun san gwamnati ta gina wurinta, kuma ta bawa mutane ‘temporary allocation’. ‘Temporary’ daman kasan cewa an baka ne na wucin gadi. Amma ita wannan babbar kasuwar ta mu yanzu haka tana da shekaru 70 da ɗoriya, kamar yadda ita kuma kasuwar NPN take da shekaru 34.

Mu fa ba ma musun cewa na wucin gadi ne. Amma wucin gadin nan sai a tambaya waye mamallakin wurin a yanzu. Mu kawai Magana muke yi a kan mamallakin wurin, kar a canza, a bar masa kayansa. Mun yarda da tsarin gwamnati, za ta iya karɓar kayanta ta ce tana so, amma a mayar wa mamallakin wurin, ai ci gaba ake so, ba wai tauye haƙƙin mutane ba, ba wai haɗa husuma ba. Mulki ai dukkanmu kafin mu zo, wasu sun yi da yawa, kuma za mu bari, tun da ba za mu mutu a kai ba.

Don haka mu a tsarin da ake tafiya, a kai muke so a tafi. Mu kawai muna so a tafi a kan tsarin da ake kai. Kana da takarda, saya ka yi ko ba ka aka yi, kai dai kai ne me shago. Ka saka kaya da kanka, ko bawa wani haya, ko kuma ka bawa wani xan’uwanka ya ci abinci, amma dai kai ne me shago.

To mu a haka muke so a tafi, kuma shi ne zaman lafiya. A babbar kasuwar Potiskum, muna da shaguna sama da dubu huɗu. A kowane shago ma ka ɗauka yana ɗauke da mutane biyar. Kai akwai shagon ma da yake ɗauke da mutane sama da goma. Yanzu mutane dubu nawa ne suke cin abinci a wannan kasuwa? A ƙalla a cikin wannan kasuwa, kullum mutane sama da dubu tara ne suke cin abinci a kullum.

A hakan ma ban da Leburori. Sannan ga shagunan cikin unguwanni, ga kuma ƙananan kasuwanni na gefe. Sannan ga Kasuwar Hatsi, ga kasuwar Shanu, ga kuma kasuwar Awaki.
Yanzu waɗannan mutane sama da dubu tara ɗin nan, idan za ka basu aikin gwamnati ina za ka saka su? Amma ba ka san a ina suke kwana ba, ba ka san yaya suke ci, suke sha, suke rayuwa ba. Ba ka sani ba, ai sun rage wa gwamnati aiki. Sannan a hakan za ka ga mutum yana da mata biyu ko uku, kuma yana da ‘ya’ya sama da goma, kuma shi yake ciyar dasu. Yanzu waɗannan ba su rage wa gwamnati aiki ba?

NEPTUNE HAUSA: Wane ƙira kake dashi ga su waɗannan masu shaguna da aka musu wannan barazana na raba su da shagunansu?

ALHAJI NASIRU MATO: Ƙira na gare su shi ne su kwantar da hankalinsu, sannan su kai hankali nesa. Don yanzu wallahi idan wani ka ƙwace masa shagonsa wallahi zai iya mutuwa, saboda hawan jini zai buge shi. Nan ne inda ya dogara da shi a rayuwarsa gaba ɗaya, da shi da iyalansa. Su kwantar da hankalinsu, a matsayinmu na shugabanni, za mu bi musu haƙƙinsu. Akwai abin da ake kawar da shi saboda maslahar al’umma. Yanzu gida na ai na kwanciya ne, idan wani abu ya taso wanda zai taimaki al’umma, kuma dole sai na ba da gida na, wallahi zan fita don a taimaki al’umma.

Sannan muna ƙara godiya ga dukkan ‘yan kasuwa, da suka kasance masu biyayya ga shugabanni. Saboda sun san muna ƙoƙarin kwatanta gaskiya. Idan muka yi ƙira, suna amsa wa. Idan muka ce a zo, suna zuwa, sannan idan kuma muka ce a tsaya suna tsayawa. Wannan babbar nasara ce. Sannan muna ƙara ƙira ga dukkan ‘yan kasuwa da su ci gaba da riƙe amana da cin halas a dukkan kasuwancin mu. Sannan mu guji haram.

NEPTUNE HAUSA: Mun gode.

ALHAJI NASIRU MATO: Nima na gode.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Shugabannin soja na yankin Sahel suna gudanar da taro a Nijer, yayin da ECOWAS ke taro a Najeriya

Published

on

Shugabannin soja na yankin Sahel suna gudanar da taro a Nijer, yayin da ECOWAS ke taro a Najeriya

Shugabannin soja na yankin Sahel suna gudanar da taro a Nijer, yayin da ECOWAS ke taro a Najeriya

Afirka ta Yamma mai rarrabuwan kai ta gudanar da tarukan ƙolin shugabannin ƙasa guda biyu a ƙasashe daban-daban biyu a ƙarshen makon, inda aka gudanar da taro farko ranar Asabar a Nijar tsakanin shugabannin mulkin soja na yankin Sahel.
A gefe guda kuma za a gudanar da wani taron ƙoli ranar Lahadi a Najeriya inda shugabannin sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar tattalin arziƙin yankin ta ECOWAS za su hallara.

Taron ƙolin da ake yi yau Asabar a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, zai kasance karo na farko tsakanin shugabannin sojojin sabuwar ƙungiyar haɗin kan yankin Sahel wato Alliance of Sahel States ko kuma AES.

Mali, Burkina Faso da Nijar su ne suka kafa yarjejeniyar kare juna a watan Satumba, waɗanda suka bar babbar ƙungiyar ECOWAS a cikin watan Janairu.

Ficewar su daga ECOWAS, wani ɓangaren ya samo asali ne daga zargin da suke yi cewa Paris tana yiwa ƙungiyar katsalandan kana ba ta ba da taimakon da ya kamata a yaƙi da masu iƙirarin yaƙin jihadi.

Ficewar ta sa ƙasashen uku sun janye kansu daga Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, suka kori sojojin Faransa masu yaƙi da masu iƙirarin jihadin kana suka juya zuwa ga ƙasashen da suke ƙira da aminan gaskiya, da suka haɗa da Rasha da Turkiya da kuma Iran.

KU KUMA KARANTA:Shugabannin Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa ƙungiyar haɗaka

Idan aka yi la’akari da munanan tashe-tashen hankula na ‘yan jihadi da ƙasashen uku ke fuskanta, “yaƙin da ta’addanci” da “ƙarfafa haɗin gwiwa” za su kasance kan ajandar taron ƙolin na yau Asabar, a cewar fadar shugaban ƙasar Burkina Faso.

Taron ƙolin da za a gudanar ranar Lahadi a Abuja zai ba shugabanni a ƙasashen ECOWAS damar tattaunawa a kan irin alaƙa da za su ƙulla da ƙungiyar ta AES.

Bayan wasu tarurrukan da suke yi tsakanin ƙasashe biyu, shugabannin uku na yankin Sahel sun yi taro a karon farko tun bayan da suka hau karagar mulki ta hanyar juyin mulki tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.

Continue Reading

Labarai

Nan da 2030 za a fuskanci matsananciyar yunwa a Nijeriya — Majilisar Ɗinkin Duniya

Published

on

Nan da 2030 za a fuskanci matsananciyar yunwa a Nijeriya — Majilisar Ɗinkin Duniya

 

Nan da 2030 za a fuskanci matsananciyar yunwa a Nijeriya — Majilisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar ‘yan Najeriya miliyan 82, kimanin kashi 64 na ‘yan ƙasar ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekarar 2030.

Haka kuma MƊD ta yi ƙira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.

Jaridun Najeriya sun ambato jami’in Majalisar Ɗinkin Duniyar, Taofiq Braimoh – wanda ya wakilci kodinetan ayyukan jin ƙai na hukumar abinci da ayyukan noma na majalisar na bayyana haka lokacin da yake jawabi kan matsalolin ƙarancin abinci a taron ƙaddamar da shirin bunƙasa ayyukan noma na ‘CropWatch’ a birnin Abuja.

KU KUMA KARANTA:Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 da aka yi garkuwa da su

Mista Braimoh ya ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa don magance matsalar.

“Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda Jaridun ƙasar suka ambato Braimoh na bayyanawa.

Ya ci gaba da cewa matsalar rashin abinci da ƙasar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ƙwari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma barazana a ƙasar.

Hasashen na Majalisar Ɗinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama haƙura da sayen abincin da suka saba ci.

A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ƙididdigar ƙasar ta ce farashin abinci a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.

Continue Reading

Labarai

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Published

on

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Yarjejeniyar Auren Jinsi: Gwamnatin Najeriya za ta kai jaridar Daily Trust kotu

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta maka jaridar Daily Trust a kotu, tare da shigar da ƙorafi game da ita, a gaban ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya saboda abin da ta ƙira ”yaɗa kalaman neman tayar da rikici da karya aikin jarida”

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tana sane da yadda a cikin ‘yan watannin baya, jaridar Daily Trust ke yaɗa labaran da ke neman gogawa gwamnatin kashin kaji.

Da ya ke magana a wajen wani taron manema labarai a ranar Asabar, ministan yaɗa labaran ya kafa hujja da labaran da jaridar Daily Trust ta wallafa a game juyin mulkin Nijar, da wanda ya ce jaridar ta rubuta a kan shirin sauya sunan titin Murtala Muhammad da ke Abuja zuwa Wole Soyinka da kuma na baya bayan nan a game da sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi amincewa da auren jinsi.

KU KUMA KARANTA: Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraƙi

Ya yi bayanin cewa a dukkan labaran, gwamnatin ta gano yadda jaridar ta bayar da rahoto ba tare da gabatar da hujja ko shaidun zargin da ta yi ba, lamarin da kuma gwamnatin ke kallo a matsayin wani yunƙuri na wallafa ƙarya domin tunzura jama’a.

Ya ce: ‘’Ba mu taɓa tunanin Daily Trust da mutanen da ke da ita za su kai wannan mataki ba wajen neman tayar da rikici a ƙasar nan, ta hanyar zargin cewa gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar tallata auren jinsi. Wannan tsabar zalunci ne saboda babu wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.’’

Ministan ya koka da yadda wannan labarin ya janyo huɗuba mai zafi daga wasu malaman addini da kuma jefa jama’a cikin halin ɗarɗar, wanda kuma ya ce jaridar ce ta janyo.

KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Saboda haka, ministan ya ce ‘’Gwamnatin tarayya za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su, domin neman haƙƙi a kotu.’’

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like