Za mu ci gaba da ayyukan da muka faro a shekaru huɗu da suka gabata – Gwamnan Yobe

0
302

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta faro a shekaru huɗu da suka gabata domin inganta ci gaban jihar Yobe tare da kasancewa jiha mafi bunƙasa a Najeriya.

Gwamna Buni ya bayyana haka ne da yammacin ranar Laraba a Damaturu, lokacin da yake jagorantar taron ƙaddamar da majalisar kwamishinonin sa a wa’adi na biyu.

Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a wa’adin mulkinsa na farko a fannin inganta kiwon lafiya, samar da gidaje, farfaɗo da harkar ilimi, samar da wutar lantarki a yankunan karkara, shimfida tituna, ayyukan jinƙai, da sauransu. Sannan ya kuma ce gwamnatin ta samar da ci gaba mai ma’ana, duk da yadda aka fuskanci ƙalubalen annobar korona (COVID_19) tare da karayar tattalin arziƙin duniya koma bayan da ya mamaye fiye da rabin shekaru huɗu na farko na mulkin sa.

Gwamna Buni ya buƙaci majalisar zartaswar jihar su tashi haiƙan wajen fuskantar ayyukan ci gaban jihar wanda yake a gaban su tare da ɗora jihar Yobe a haƙiƙanin alƙiblar da ta dace domin kai wa ga matsayi mafi girma a wa’adinsa na biyu na mulki.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Yobe ya ba da tallafin kuɗi a mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

“Ya kamata mu mai da hankali kan ci gaban wannan jihar, kuma mu fahimci cewa babu wani abu da ya hau kanmu kamar tsayuwar mashi wajen tabbatar da mafarkin da al’ummar Yobe suke da shi wajen ganin mun bunƙasa ci gaban jihar.” In ji shi.

Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su yi aiki tare, da jaddada cewa kowace ma’aikata kuma kowane kwamishina ɓangare ne mai muhimmanci a tsarin tafiyar da harkokin gwamnati.

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa zai kammala dukkan ayyukan da ya fara a wa’adin sa na farko tare da ƙaddamar da sabbi da aiwatar da su domin amfanin al’ummar jihar.

A wani labarin kuma, Gwamna Buni ya sanar da naɗin Sakataren Gwamnatin jihar Yobe (SSG), Alhaji Baba Mallam Wali da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin (COS), Alhaji Abdullahi Gashu’a a matsayin SSG da COS.

Leave a Reply