Gwamna Sani ya yabawa sojojin da suka kawar da masu tayar da ƙayar baya a Kaduna

1
307

Gwamna Uba Sani na Kaduna a ranar Juma’a ya yabawa dakarun sojojin Najeriya bisa yadda suka tozarta tare da kawar da masu aikata laifuka a jihar.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Lawal, ya bayyana haka a Kaduna, inda ya ce gwamnan ya yabawa sojojin musamman kan yadda suka fatattaki ‘yan bindiga a ƙauyukan Kagarko-Iche, Takalafiya, Gidan Maƙeri da Jangala a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar.

“Nasarar da aka samu na da nasaba da ƙaruwar sa ido da kuma matakan haɗin gwiwa na jami’an tsaro,” in ji Lawal.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ce sun ceto mutum 40 daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara

Ya kuma ƙara da cewa gwamnan yana ba da tabbacin gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin tunkarar matsalolin tsaro da ke kunno kai.

Gwamnan ya yi nuni da cewa yawan jibge sojoji zuwa yankunan da ake fama da rikici a jihar ya haifar da raguwar ‘yan fashi da garkuwa da mutane tare da dawo da harkokin tattalin arziƙi a yankunan.

1 COMMENT

Leave a Reply