Ranar zuma ta duniya: Amfani da sirrikan dake tattare da zuma

1
742
jar of honey with honeycomb on wooden table

Yau ranar zuma ta duniya. Neptune Hausa ta binciko muku amfanin zuma ga ɗan adam. Ku biyo mu don sanin sirrikan dake tattare da wannan halitta ta Ubangiji.

Zuma dai kamar yadda muka sani wata halitta ce mai matuƙar tasiri a rayuwar ɗan adam. Kasantuwar ƙudan zumar yana cin furanni da kuma wasu lokutan itatuwa daban daban, hakan ne ma kashin sa da yake fitar wa ake da yakinin yana magunguna da dama a cikin jikin ɗan adam.

Mutane dai suna amfani da ruwan zumar a matsayin abinci ko magani ga cututtuka da dama. Haka ma dai an ambaci zuma a wurare da dama a cikin alkur’ani mai girma saboda muhimmancin ta.

  1. Tana taimaka ma mai-mura, tari, atishawa da sauran matsalolin sanyi.
  2. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
  3. Tana rage nauyin ƙiba. Shan ruwa mai`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage ƙiba.
  4. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
  5. Tana sauƙaƙa narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
  6. Maganin gudawa ce.
  7. Tana karfafawa garkuwar jiki.
  8. Tana gyara fata da rage ƙurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
  9. Maganin gyambon ciki – Ulcer.
  10. Tana kara kuzari.
  11. Zuma na kare mutane daga kamuwa da cutar siga wato Diabetes da turanci sannan kuma yana hana tashin cutar wa mutanen da ke fama da shi.
  12. Zuma na maganin matsalolin da ke kama ido kamar jan ido, kaikayin ido, kumburin ido da sauransu.
  13. Zuma na rage yawan mantuwa musamman matan da suka daina haihuwa.
  14. Zuma na ƙara kaifin basira da riƙe karatu musamman a yara.
  15. Yana kuma maganin cutar Ulcer.
  16. Zuma na taimaka wa mutanen(maza ko mata) dake fama da matsalar rashin haihuwa.
  17. Zuma na kuma maganin ciwon ciki.
  18. Ana amfani da zuma wajen gyaran gashi.
  19. Zuma na da amfani wajen ibadar aure da lafiyar ma’aurata.
  20. Ana amfani da zuma a maimakon sukari wajen sawa abin sha ɗanɗano.

1 COMMENT

Leave a Reply