ISWAP ta kashe mutane uku da jikkata sojoji takwas a Borno

0
241

Aƙalla ‘yan gudun hijira guda uku ne aka kashe tare kuma da jikkata wasu 13 ciki har da sojoji guda takwas a wasu mabambantan hare-hare da ƙungiyar ISWAP ta kai ƙaramar hukumar Damboa na jihar Borno.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan gudun hijira guda huɗu da ke zama a sansanin Lowcost a Damboa suka fita domin neman itacen hura wuta lokacin da mayaƙan suka buɗe musu wuta, inda suka kashe uku nan take yayin da sauran mutane kuma suka tsere da raunuka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun da farko ISWAP ɗin sun jikkata wasu sojoji da kuma fararen hula yayin wani hari da suka kai yankin Talala a ranar Talata duk a Damboa.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe mayaƙan na ISWAP da dama a wani hari da suka kai musu.
Majiyar ta ce wani jrgin sama na sojoji ya je Damboa a jiya Alhamis, inda ta ɗebo sojoji da suka jikkata zuwa Maiduguri domin yi musu magani.

Leave a Reply