Gwamnatin Kaduna ta dawo da malaman firamare 1,288 da ta kora

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da a dawo da Malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki a watan Yunin 2022 bayan kammala jarrabawar tantancewa.

Hajiya Hauwa Mohammed jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna SUBEB ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar Laraba.

Ta bayyana cewa Malamai 1,266 ne jarabawar cancantar ta shafa, yayin da wasu 22 kuma aka cire su daga cikin albashin gwamnati bisa zargin da ake musu na rashin gaskiya.

A watan Yunin 2022 hukumar ta kori Malaman Firamare 2,357 saboda ka sa cin jarabawar cancanta aka musu. Hukumar ta bayyana cewa, daga cikin adadin, an kori Malamai 2,192 saboda rashin cin jarabawar da suka yi, yayin da aka kori Malamai 165 saboda rashin aikin yi.

KU KUMA KARANTA: Malamai sun yiwa Tinubu da Najeriya addu’a zagayowar ranar haihuwarsa

Sai dai wasu daga cikin Malaman da abin ya shafa, sun koka da cewa sun rubuta jarabawar sun ci jarabawar, amma har yanzu an kore su daga aiki, yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa ba su da lafiya a lokacin jarabawar tare da bayar da shaida.

Wasu daga cikin ma’aikatan da abin ya shafa sun yi iƙirarin cewa an yi garkuwa da su a lokacin, yayin da wasu ke iƙirarin cewa an dakatar da su ne saboda tabbatar da satifiket ɗinsu, yayin da wasu kuma ke ikirarin cewa ma’aikatan gwamnatin tsakiya ne, kuma a dalilin haka aka hana su rubuta jarabawar.

“Bayan ta yi nazari tare da tantance ƙorafe-ƙorafen su, gwamnatin jihar ta amince da mayar da Malamai 392, waɗanda suka rubuta kuma suka ci jarabawar, da ma’aikatan gwamnatin tsakiya 515 waɗanda a hukumance aka cire su daga jarabawar.

“Sauran su ne: Malamai 298, waɗanda aka tabbatar da cewa ba su da lafiya a lokacin da aka yi jarabawar, da kuma malamai 61 da aka yi garkuwa da su ko kuma suka yi hatsari da Sakatarorin Ilimin nasu suka tantance.

“Har ila yau, an mayar da malamai 22, waɗanda aka cire na dindindin daga cikin albashin ma’aikatan da ba su da wata hujja, waɗanda adadinsu ya kai 1,288 da aka mayar da su bakin aikinsu.

Don haka kakakin ya shawarci duk malaman da abin ya shafa da su tattara takardun mayar da su daga Sakatarorin Ilimin nasu cikin gaggawa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *