Hukumomin Saudiyya da Najeriya da kasar Qatar sun sanar da ganin jinjirin watan Ramadan tun a ranar Laraba kuma hakan ne yasa aka fara azumin watan Ramadan daga yau Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Saudiyya cewa, a yammacin jiya Laraba ne kotun kolin ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ranar Laraba ce za ta kasance ranar karshe na watan Sha’aban, wanda ke gabanin watan Ramadan, ranar Alhamis ne ɗaya ga watan Ramadan.
Haka zalika a Najeriya Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakbar ne ya bada sanarwar ganin watan tare da umartar ‘yan kasar da su tashi da azumin Ramadan a ranar Alhamis.
KU KUMA KARANTA: An Bukaci Al’ummar Musulmi Da Su Yi Aiki Da Darussan Ramadan
An kayyade watan Ramadan bisa kalandar Musulunci, wanda ke farawa a farkon ganin wata. Jami’ai a yankunan Falasdinawa da na Masar suma sun sanar da cfara azumin watan Ramadan a ranar Alhamis.
A duk tsawon watan Ramadan al’ummar musulmi a faɗin duniya na gudanar da azumi kafin fitowar alfijir, zuwa lokcin faduwar rana.
Azumi ya ƙunshi kamewa daga ci, sha, da kuma jima’i don samun taron Allah “takawa”, da kuma kusanci zuwa gare shi.