Yadda ɗan El-Rufai ya lashe kujerar majalisar tarayya a Kaduna

0
273

El-Rufai Muhammad Bello na jam’iyyar APC, ya lashe zaɓen mazaɓar Kaduna ta arewa da ke jihar Kaduna da ƙuri’u 51,052.

Farfesa Mohammed Magaji Garba na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma jami’in hukumar INEC da yayi aikin zaɓen ya sanar da sakamakon zaɓen a ɗakin taro na Magajin Gari da ke Kaduna ranar Litinin.

Garba ya ayyana Bello a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya doke abokin takararsa na kusa, ɗan takarar da ke wakiltar yankin, Malam Suleiman Samaila Abdu na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 34, 808, Malam Aliyu Mohammed Ahmad na NNPP ya zo na uku da ƙuri’u 10,148 sannan Shehu Mohammed Faisal na jam’iyyar Labour (LP) ya samu kuri’u 7,531.

KU KUMA KARANTA: Yadda Melaye, da wasu ‘yan jam’iyya suka fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓe a fusace

“El-Rufai Mohammed Bello bayan ya cika sharuɗɗan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.”

Jami’in zaɓen ya ce mazaɓar na da masu kaɗa ƙuri’a 369,428 . Ya ce daga cikin masu kada ƙuri’a 369, 428, 110, 269 7 ne aka amince da su a zaben, yayin da 106, 073 suka samu sahihin kuri’u.

Leave a Reply