‘Yan ta’adda sun kaima tawagar jami’an EFCC, waɗanda ke bakin aikin sa ido a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya farmaki a ranar Asabar a kusa da fadar shugaban ƙasa a ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.
Harin dai ya biyo bayan kama wani mutum ne da ake zargi da kitsa tsarin siyan ƙuri’u a rumfar zaɓe da ke makarantar Science Primary School, Bwari.
Rundunar ta kama wanda ake zargin, wanda aka ce ɗan kimanin shekaru 30 ne, kuma ta tattaro jerin sunayen waɗanda suka ci gajiyar kuɗin da ya riga ya biya, ta wata manhajar banki ta yanar gizo.
A dai dai lokacin da ake ɗauke wanda ake zargin daga sashin kaɗa ƙuri’a ne ‘yan barandan suka kai hari, inda suka farfasa gilashin motar sintiri na Hukumar.
KU KUMA KARANTA: Yan sanda sun kama dattijo da ke yiwa ‘yan ta’adda maganin bindiga
Sai dai sun koma maɓoyarsu ne bayan jami’in hukumar ya mayar da martani ta hanyar yin harbin gargaɗi, kafin daga bisani jami’an rundunar haɗin gwiwa da suka haɗa da hukumar tsaro ta farin kaya, ‘yan sandan Najeriya, da sauran su suka isa wurin.
Nan take aka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Bwari.
Hakazalika, tawagar jami’an EFCC da ke aikin sa ido kan zaben da ke Unit 001, Makarantar Firamare ta Mann da ke bayan mahaɗar Chorobim, wasu wasu bakar fata guda biyu kirar Prado SUV da wani farar fata Hilux ne suka harɓe a wajen rumfar zaɓe, wadanda ake zargin suna sayen kuri’u.
Hukumar EFCC ta mayar da martani, inda ta tilasta musu tserewa daga wurin. An kai rahoton faruwar lamarin ga DCP Operations, Haruna Femi, a rundunar ‘yan sandan jihar Imo.
[…] KU KUMA KARANTA: An kai wa jami’an hukumar EFCC hari a Abuja da Imo […]
[…] KU KUMA KARANTA: An kai wa jami’an hukumar EFCC hari a Abuja da Imo […]