Buhari ya ba da umarnin a daina karbar tsohuwar takardar kuɗi ta N1000 da ta 500, yayi rangwame kan 200

0
305

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a cigaba da karɓar tsohuwar takardar kuɗi ta N200 a kasuwannin hannayen jari, wanda ya zama doka daga ranar 10 ga Fabrairu, 2023 zuwa 10 ga Afrilu, 2023.

KU KUMA KARANTA: Sauyin Takardun Kuɗi: Shugaba Buhari zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani shiri jawabinsa da yayi, aka watsa kai tsaye a faɗin kasar a ranar Alhamis, 16 ga Fabrairu, 2023.

Shugaban ya ce tsohuwar takardar N200 da sabuwar takardar da ta haɗa da sabbin N500 da N1,000 za su yi aiki a lokaci guda.

Tsohuwar takardar N500 da N1,000 za a daina karɓa domin sun daina zama doka.

Leave a Reply