Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wani matashi mai suna Lot Bitrus ɗan shekara 24 bisa zarginsa da kai wa ayarin motocin gwamnan jihar Ahmadu Fintiri, da uwargidansa Hajiya Lami Fintiri hari a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa an kai wa Hajiya Fintiri hari ne a garin Muchala da ke yankin Mubi a jihar, yayin da wasu ‘yan daba suka yi ta jifan ayarin motocinta a lokacin da suke shiga ƙauyen domin halartar taron matan Katolika.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar a jihar, Suleiman Nguroje ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa tura jami’an tsaro da suka yi domin kai farmaki kan ‘yan daba ya kai ga cafke Bitrus.
KU KUMA KARANTA:Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje
Ya ce za a ƙara bincikar wanda ake zargin kan lamarin. “Wanda ake zargin, Lot Bitrus, ɗan shekara 24, mazaunin unguwar Muchalla, an kama shi ne a maɓoyarsa da ke wani wuri mai nisa na ƙauyen Muchalla, ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa, yanzu haka yana tsare,” inji shi.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sikiru Akande ya bukaci ‘yan siyasa a jihar da su ja kunnen magoya bayansu domin ba za a lamunci duk wani nau’in hari a jihar ba.
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka kama matashin da ake zargi da kai hari kan ayarin motocin matar gwamna […]