‘Ta kashe aurenta don ta auri tsohon saurayin ‘yarta’

1
312

Wata mata ‘yar Kano mai suna Malama Khadija daga ƙaramar hukumar Rano, ta kashe aurenta sannan ta auri wanda ya ƙi auran da ‘yarta.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito a ranar Laraba, ‘yan uwan ​​Khadijah sun zargi kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Rano da auren ‘yarsu ba tare da yardarsu ba, kuma ba su ma san inda take ba.

Sai dai da take magana da gidan rediyon, Freedom Radio, Malama Khadija ta bayyana cewa, tana cikin ƙoshin lafiya kuma tana rayuwa cikin jin daɗi da sabon mijin nata.

An ruwaito ta bayyana cewa a lokacin da ɗiyarta Aisha ta yanke shawarar ba za ta auri mutumin ba, sai ta ji bai kamata su biyu su rasa shi ba don haka ta yanke shawarar tuntubar danginsa ta aure shi.

KU KUMA KARANTA:Hukumar Hisbah ta kama mata da maza 23 a wuraren da basu daceba a Nasarawa GRA

Ta ce, “Ban yi shi da jahilci ba,na tuntuɓi malamai suka ce ba a haramta ba. da na tuntube shi, ya amince, amma iyayena da ’yan uwana sun ƙi su amince, hakan ne ya sa na yanke shawarar zuwa ofishin Hisbah kuma muka yi aure cikin farin ciki yanzu.” in ji ta.

Kawun Malama Khadija, Abdullahi Musa Rano, ya bayyana abin da ta yi a matsayin abin kunya, ya ce, “Ta matsa wa mijinta ya sake ta don kawai ta auri mutumin.

“Ba za mu iya yin wannan abin kunya a cikin iyalinmu ba, wanda shine dalilin da ya sa muka ƙi haɗa su auren.

“Ba mu ji daɗin abin da Hisbah ta yi ba, kuma muna ba da rahoton dawo da ‘yar mu,muna son babban kwamanda da gwamnatin jihar su duba lamarin.”

1 COMMENT

Leave a Reply