Kotu ta umurci budurwa ta biya saurayinta N150,000 bayan ta karɓi kuɗin mota N3000 ta kuma ƙi amsa gayyatarsa

0
496

Kotu ta umarci wata mata da ta karɓi naira dubu uku kuɗin mota wajen saurayinta domim ta ziyarce shi, amma daga baya ta kashe wayarta, ta ƙi zuwa, da ta biya saurayin kuɗi naira dubu N150,000, bayan da saurayin ya kai ƙarar budurwa tasa kotun.

Kotun da ke zama a jihar Enugu ta yanke hukuncin ne dan koya wa mata masu yaudara darasi, domin shari’ar ta zamo izina ga wasu matan.

KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum shaƙe budurwarsa saboda cin amana, ya kuma cinna wa kansu wuta

Wani Lauyan Najeriya mai suna @Egi_nupe_ a shafinsa na tweeter, ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce matar ta kashe wayarta bayan ta karɓi kuɗin kuma hakan ya fusata saurayin nata.

Mutumin da bai ji daɗin abin da ya faru ba, ya garzaya kotun shari’ar Enugu inda ya yi nasara.

A cikin hukuncin, alkalin kotun ya ce abin da matar ta aikata yaudara ne.

Adadin tarar da aka ɗora wa matar, an yi ne don ya zama izina ga sauran mata masu irin wannan dabi’a ko tsare-tsare na yaudara.

Leave a Reply