Yadda aka tsinci gawar ma’aurta a kan gadon aurensu a Kano

0
306

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne aka tsinci gawar wani magidanci mai suna Sulaiman Idris mai shekaru 28 tare da gawar matarsa ​​Maimuna Halliru mai shekaru 20 a kan gadon aurensu.

A wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce ma’auratan ba su fito daga gidansu ba, tun ranar Laraba 02/01/2023, inda suka shafe kimanin awa 23 a ɗaki.

Ya ce “A ranar Litinin, 03/01/2023 da misalin ƙarfe tara na safe, an samu rahoto daga ƙauyen Kwa, na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano cewa wasu ma’aurata, Sulaiman Idris, da matarsa Maimuna Halliru, ba su fito daga gidansu ba tun ranar 02/01/2023 da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Binciken farko, an gano cewa ma’auratan da suka mutu sun kunna wuta don dumama ɗakinsu saboda sanyin da su ke ji, kuma ko’ina a kulle, dalilin haka hayaƙi ya balbale su a lokacin da suke barci.

“Lokacin da kakar mijin buɗe ƙofar ɗakinsu da ƙarfi, sai ta tarar da ma’auratan basa motsi a kan gadon su, ta kuma iske da ragowar hayaƙi a ɗakin.

“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ​ya umurci tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Ahmed Hamza,DPO na ‘yan sandan reshen Dawakin Tofa da suje suga wurin, inda suka ka kai ma’auratan asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano kuma a nan wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci al’ummar jihar Kano da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da wuta, da kuma lantarki, sannan a kula da ɗaukar matakan kariya saboda lokacin sanyi yana da alaƙa da haɗarin gobara.

Leave a Reply