Nasara ta zata bai wa ibo damar shugabancin Najeriya – Atiku

0
241

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin sanya tashar jiragen ruwan Onitsha ta yi aiki idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban, ya yi alƙawarin ne a ranar alhamis a taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP da aka gudanar a Awka jihar Anambra.

Ya ce: “Da isowarmu a yau mun ziyarci Gwamna Soludo kuma ya ce min ya yi imani cewa zan yi aiki idan na yi nasara.

“Don haka, ya buƙace ni da in sake gina dukkan hanyoyin tarayya da kuma shawo kan matsalar zaizayar kasa a jihar, saboda ana daukar Anambra a matsayin hedikwatar zaizayar ƙasa a ƙasar nan.

Kuma na yi masa alƙawari zan yi hakan.

“Na kuma yi alƙawarin yaye kogin Neja kuma in tabbatar da cewa tashar jiragen ruwa ta Onitsha ta fara aiki, idan kun zaɓi PDP a zaɓe mai zuwa.

KU KUMA KARANTA:Dala Biliyan 10 zan ware don inganta rayuwar matasa tare- Atiku Abubakar

“Za mu kuma inganta jihar don samar da ayyukan yi ga matasan mu,” in ji shi.

Atiku ya ce shi ne zai zama matakin tabbatar da shugabancin Igbo idan aka zabe shi a shekarar 2023.

“Zan zama matattakalar shugabancin Igbo. Na nuna hakan ta hanyar ayyukana ne domin wannan shi ne karo na uku da zan yi takara da ɗan kabilar Ibo a matsayin abokin takarata.

“Idan kuna son samar da shugaban kasa, to ku zaɓi Atiku/Okowa.

“Na gode muku da wannan kyakkyawar tarba, kuma mun yi alkawarin ba za mu ba ku kunya ba,” in ji Atiku.

Shima da yake jawabi, Gwamna Ifeanyi Okowa, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, ya yaba wa shugabannin jam’iyyar bisa gagarumin yaƙin neman zaɓe na al’ummar jihar Anambra.

Ya ce “Muna ƙira gare ku da ku zaɓi PDP a babban zaɓe.
“Ɗan takararmu na shugaban kasa, Atiku, shi ne ya fi kowa gogewa a cikin dukkan ‘yan takarar da ke takara, kuma ya ƙuduri aniyar sauya fasalin Najeriya,” in ji Okowa.

A nasa jawabin, Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya bukaci jama’a da su kaɗa ƙuri’a ga jam’iyyar PDP, inda ya bayyana jihar Anambra a matsayin jihar PDP ba ta APGA ba.

“PDP ta fara ne a Anambra tare da shugabanmu, Dr Alex Ekwuene, don haka Anambra ta PDP ce ba APGA ba.
APGA ɗan PDP ne kuma nan gaba za mu dawo da APGA gidansu wato PDP.

“ ‘Yan ƙabilar Igbo, musamman a Anambra, masu ruwa da tsaki ne a Najeriya, domin babu wani ƙauye da za ku je a ƙasar nan da ba za ku ga ɗan ƙabilar Igbo ba. Wannan ya sa sun fi zama ‘yan ƙasa.

“Ina rokon ku da ku zaɓi PDP saboda muna da ƙwararre mai cancanta, wanda ɗan kasuwa ne kamar ku, kuma surikinku. Wani lokaci surikinku ya fi ɗanku.

“Don haka, ku je ku karɓi katunan zaɓe na dindindin ku zaɓi Atiku/Okowa. Wannan tawagar za ta magance matsalolin tsaro na Najeriya, da daidaitawa da kuma sauya yanayin kasar nan,” in ji shi.

A nasa jawabin, Farfesa Obiora Okonkwo, darakta janar na yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa, ya bukaci jama’a su zaɓi Atiku a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Okonkwo ya ce nasarar da ya samu a rumfunan zaɓe, za ta ba igbo damar shugaban cin kasar .

Leave a Reply