An gano tarkacen takardun kuɗi da suka lalace a shara

1
302

Daga Maryam SULAIMAN, Abuja

Rahotanni sun ce an gano wasu makudan kuɗi na Naira da ba a bayyana adadinsu ba, a wani ɗakin ajiyar kaya.

Wannan sabon cigaban ya zo ne, kasa da wata guda bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bayyana shirin sake fasalin takardun kudi na N200, N500 da N1000 da kuma kaddamar da sabbin takardun a makon jiya da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.

A cewar Crimechannels, kudin ya kasance a cikin jakunkuna da yawa a ajiye na tsawon lokaci a cikin yanayin danshi, wanda ya haifar da lalacewarsu.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta na yanar gizo,an ga mutane a cikin faifan bidiyon,suna bincika kowace jaka, tare da fatan ganin kuɗin da basu kai ga lalacewa ba, sai dai haƙarsu ba ta cimma ruwa ba domin kuɗin duk sun riga sun lalace.

KU KALLI BIDIYON ANAN:https://fb.watch/h6L3QUBIW2/

A halin da ake ciki kuma, a cewar babban bankin na CBN, kudaden da ba a kai ga sanya su cikin bankin sun karu daga N108.67billion zuwa N2.84t a watan Oktoban 2022 daga Naira Tiriliyan 2.73 a watan Satumba, kamar yadda ƙididdigar kuɗaɗen ta bayyana.

Bayanai na babban bankin, kuɗin da ke wajen bankunan, sun karu da kashi 11.07 na Shekara-shekara daga Naira tiriliyan 2.54 da aka ruwaito a shekarar 2021.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yankewa IGP hukuncin ɗaurin watanni 3 a gidan yari

Ƙididdigar kuɗadmɗe, ta nuna cewa kuɗaɗen da ke wajen bankunan, sun kai matsayin mafi girma na Naira tiriliyan 2.84 a watan Oktoba.

Yayin da yake kare kan shi akan matakin da ya ɗauka na sake fasalin kuɗin Naira, babban bankin a watan Oktoba, ya bayyana cewa wasu mutane na tara makudan kudade a wajen banki.

Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “akwai adadin masu yawa na takardun kuɗi da jama’a ke ke ajiyarsu a wajen banki, inda alƙaluma suka nuna cewa, sama da kashi 85 bisa 100 na kudaden da ke yawo a kasuwannin duniya, ba safai suke a bankunan kasuwanci ba.

“Kamar yadda a ƙarshen Satumba 2022, bayanai da ake samu a babban bankin na CBN, sun nuna cewa Naira tiriliyan 2.73 daga cikin Naira tiriliyan 3.23 da ake yaɗawa, suna wajen bankunan kasuwanci a faɗin ƙasar nan; kuma ana zaton suna hannun jama’a.

“A binciken , kuɗaɗen da ke gudana sun ninka fiye da ninki biyu tun daga 2015; ya tashi daga Naira Tiriliyan 1.46 a watan Disamban 2015 zuwa Naira Tiriliyan 3.23 a watan Satumban 2022. Wannan lamari ne mai matukar tada hankali, da ba za a bari ya ci gaba ba.” inji shi.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa kudin shiga (CIC) ya karu da kashi 11.22 bisa dari zuwa Naira tiriliyan 3.3 a watan Oktoban 2022 daga Naira tiriliyan 2.97 a shekarar 2021.

Wani Manazarci, kuma Shugaban Kungiyar Abokan Ciniki ta Najeriya (BCAN), Dr. Uju Ogubunka, ya danganta ƙaruwar CIC da kuɗaɗen da ‘yan siyasa ke kashewa wajen zaben fidda gwani na 2023.

Kalli bidiyo ta hanyar mahaɗin da ke ƙasa: https://fb.watch/h6L3QUBIW2/

1 COMMENT

Leave a Reply