Da rana tsaka a jiya Lahadi, ‘yan bindiga suka tare hanyar Jibia zuwa Katsina, inda suka harbe direban motar Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA), suka kwashe mutum 16 suka yi awon gaba da su.
Cikin waɗanda suka tsira a harin sun bayyana cewa a daidai garin Kodobe zuwa Farun Bala suka yi arba da maharan ɗauke da muggan makamai, inda suka bude masu wuta, suka harbe direban nan take.
Wani bidiyo da mazauna ƙauyen da ya faru suka ɗauka, ya nuna yadda direban motar da ba a iya tantance shi ba zuwa yanzu, yake kwance cikin jini da kuma wasu daga cikin fasinjoji.
Majiyar ta shaida mana cewa, maharan sun yi awon gaba da wasu daga cikin matafiyan da adadin su ya kai mutum 16, yayin da wasu suka samu raunuka. An kai su asibiti don kula da lafiyarsu.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, gwamnatin Jihar Katsina da jami’an tsaro, ba su ce komai ba a kan harin.