Kungiyar Noman Zamani Ta NAMCON Ta Kaddamar Da Shugabannin Reshen Jihar Katsina

1
373

Daga, IMRANA ABDULLAHI.

KUNGIYAR Noman Zamani ta Najeriya (NAMCON), reshen Jihar Katsina ta gudanar da bikin Kaddamar da sabbin Shugabannin kungiyar na Shiyya-shiyya wadanda zasu Jagoranci ragamar harkokin ta a Jihar Katsina.

An gudanar da bukin Kaddamar da Shugabannin Kungiyar (NAMCON) ne a babban dakin taro tsohon gidan Gwamnatin Jihar Katsina inda Shugaban Kungiyar ta kasa, Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna, ya bayyana manufar kungiyar wacce ta ke da zummar samar da wadataccen abinci ga nahiyar Afrika baki daya.

Shugaban Kungiyar, ya fayyace cewa a kokarin da suke yi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ya zuwa yanzu, sun kaddamar da shugabannin kungiyar NAMCON a Jihohi sama da Ashirin da suka hada da Katsina.

Ya ce “zamu dauki tsarin inganta bunkasa rayuwar makiyaya da nufin bunkasa harkar Noman rani a cikin kasa”.

Ya ci gaba da bayanin cewa suna da muhimman ingantattun tsare-tsare da dama da za su kara bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

“Muna da nufin taimakawa matasan da suka kammala karatu domin su samu abin yi a kasa, saboda akwai mu da tsare-tsaren da za su taimakawa Najeriya ta tashi daga kasar da ke zaman shigowa da kayan kasashen waje zuwa kasar da ke samar da kayan amfani a cikin kasar ta”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar Noman zamani ta kasa reshen Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Maikaita Ummaru cewa ya yi da taimakon wannan kungiya Jihar Katsina za ta cimma wani babban matsayin ci gaban da duk duniya za a yi alfahari da ita, kuma hakan zai sanya ta tserewa tsara ta”.

Maikaita Ummaru ya shaidawa taron dimbin jama’a maza da mata cewa akwai tsare-tsare da dama da suke shirin kawo wa domin kasa ta ci gaba.

Wadanda aka kaddamar dai a matsayin shugabannin shiyya sun hada da ; 

Lawal Inuwa Funtua a matsayin shugaba na shiyyar Funtuwa.

Usman Umar Daura daga shiyyar Daura.

Da Abdullahi Shu’aibu a matsayin shugaban shiyyar Katsina.

Sauran sun hada da Alhaji Shehu Dan Musa, Alhaji Magaji, Alh Abubakar M Doro, Muhammad Saifullahi Safana and Alh Abdullahi Usman dukkansu daga shiyyar Katsina.

Daga shiyyar Funtuwa kuma akwai  Shu’aibu Sa’idu Musawa, Abdullahi Hatuna Musawa, Salisu A Sule Malumfashi da Umar Masari. sauran sun hada da Jafar, Fahad Sama’ila Faskari, Abdullahi Abubakar Dandume.

Daga shiyyar Daura, Bashir Aliyu Sandamu, Bashir Danjuma Mai’aduwa, Musa Salisu, Bala Dahiru, Lawal Halliru, Abdurrashid Sa’ad Mashi, Yusuf Nalado Daura, Ibrahim Sa’id Baure, Abas Mohammad Kankiya da Hamza Hamisu Karfi.

An kuma gabatar da filin yin tambayoyi ko karin haske ga shugaban kungiyar, Dokta Aliyu Muhammad Waziri inda mahalarta taron suka rika yi masa tambaya ya na kuma ba su amsa.

Jama’a dai sun bayyana gamsuwarsu da irin kokarin da kungiyar NAMCON ta ke yi domin inganta rayuwar al’umma.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here