NUJ Kaduna Ta Gudanar Da Taron Bita, Tare Da Karrama Muyiwa, Isiguzo Da Sauran Su

0
313

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta gudanar da wani taron bita na musamman tare da karrama wasu al’umma da suka hada da mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Mista Muyiwa Adekeye, Shugaban Kungiyar (NUJ) ta Najeriya, Kwamared Chris Isiguzo da sauran wasu manyan mutane da lambar yabo bisa gagarumin gudunmuwarsu.

Taron lakcan da bada lambar yabon da ya gudana a ranar Asabar din daya gabata a sakatariyar Kungiyar ta NUJ Kaduna, an shirya ne domin karawa juna sani kan mahimmancin yan Jaridu a cikin harkar Siyasa da irin rawar da zasu taka domin ci gaban Kasar Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar NUJ ta Najeriya, Kwamared Chris Isiguzo, ya bayyana akwai bukatar kasancewar yan Jaridu masu aiki da kwarewa ba tare nuna son rai a cikin aikinsu don tabbatar da an samu sauyi nagari a cikin shugabanci a kasar.

Ya ce “sai da hadin kai da zaman lafiya za a iya samun duk wani ci gaban da ake bukata a cikin kowace al’umma, don haka akwai bukatar yan Jaridu su kasance mutane masu son junansu da kyakkyawar alaka da son zaman lafiya, saboda ta hakan ne zasu iya nuni da ayyukan da za ayi koyi da su.”

“Babu shakka, yan Jaridun Kaduna na matukar Jindadin mulkin shugabancin Kungiyar karkashin Jagorancin Asma’u Yawo Halilu wadda ta yi abubuwa da dama domin inganta rayuwar mambobin kungiyar sakamakon irin hadin kan da suke bats, kuma hakan na nuni da cewa hakkin da ya rataya a wuyan yan Jaridun zasu sauke wannan nauyin ta hanyar gudanar ayyukansu yadda ya kamata.”

Hakazalika, Shugaban taron, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya jinjinawa Kungiyar da Jagorancin Asma’u Yawo bisa namijin Kokarin da ta ke na ganin cewa ta daidaita al’amura duk da kasancewar mace kuma ta farko da ta fara rike wannan matsayin a cibiyar kungiyar.

Ya ci gaba da cewa, ba karamin nauyi ba ne yake rataye a wuyan yan Jaridu da za su sauke ta hanyar ganin cewa sun gudanar da ayyukansu a cikin al’umma, musamman a irin wannan lokacin da zabe ke kunno kai kuma yan Siyasa na neman damar da zasu gana da al’umma.

Mai jawabi na musamman a wajen taron, Mista Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa dole ne duk wani dan Jarida da yake son zama yan Jaridu na kwarai, sai sun masu gaskiya, bada rahoton gaskiya da kauracewa yin aiki da jita-jita tare da samarwa da al’umma sahihan labarai na gaskiya.

Ya ce “ada Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da jituwa da Kungiyar ta NUJ Kaduna, amma a yanzu mun dinke gida domin yin aiki tare karkashin Jagorancin Hajiya Asma’u kuma za muyi kokarin ganin cewa an kara daidaita al’amura ta yadda zamu cigaba da gudanar al’amura tare musamman kasancewa Gwamnan yana sha’awar ganin an ba mata dama a cikin kowani mataki.”

Muyiwa Adekeye, ya yaba da ganin irin yadda Kungiyar ta canza salon ta duk da cewa ta na da nauyi kala biyu a kan ta wanda ya hada yin aiki karkashin Kungiyar ma’aikata da Gwamnati wanda hakan wani babban Kalubale ne a gare ta, amma idan ba ta dauki bangaranci yayin gudanar da harkokin ta, duk zata iya samun nasara a cikin ayyukanta.

Tun da farko, shugabar kungiyar (NUJ) ta Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo Halilu wadda ta bayyana wasu nasarorin da Kungiyar ta samu a cikin watanni biyar da suka gabata, ya danganta gagarumin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu ga gagarumin goyon bayan da take samu daga mambobin kungiyar da abokan huldar ta.

Ta ci gaba da cewa, sun aiwatar da shirin horarwa don inganta ƙwararrun mambobi tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin jama’a na ci gaba da gudana a jihar.

Ta ce “duk waɗannan nasarorin, an cimma musu ne saboda tallafin da muka samu daga abokan tarayya, masu girma membobinmu kuma tabbas saboda mu ma mun mai da hankali kuma muna da hangen nesa.”

“A yau jagoranmu, Dan Jarida na daya a Najeriya, Kwamared Chris Isiguzo zai kaddamar da dukkan wadannan ayyukan. Namu ne Ina muku barka da zuwa Jihar Kaduna a wannan wata na musamman.”

“Bari kuma in yi amfani da wannan dama don tabbatar wa mambobinmu cewa jindadin ku shi ne mafificin mu. Kamar yadda kuka sani, sana’ar mu tana buƙatar ci gaba da horarwa. Dole ne mu kasance masu horo kafin mu iya sanar da wasu.”- Acewar Asma’u

Leave a Reply