Shugaban NUJ Kaduna, Ta Yi Alkawarin Tallafa Wa Manufofin Aiwatar Da Tsarin Daidaiton Jinsi

0
319

Daga; USMAN NASIDI Kaduna.

SHUGABAR kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Asmau Yawo Halilu, ta bayar da tabbacin cewa kungiyar za ta bayar da gudunmawa dari bisa dari don ganin an yi nazari tare da cikakken aiwatar da daidaito tsakanin jinsi da zamantakewa na (GESI), a Jihar Kaduna.

Asmau, ta bada wannan tabbacin ne a lokacin da ta karbi tawagar kungiyar Women’s Connect Initiative da Gender Policy Unit na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da suka kai mata ziyarar neman goyon bayan sake duba manufofin KADGESI a jihar, wanda Rise Up da Public Health Institute suka tallafa mata.

A cewar shugaban kungiyar ta NUJ, galibin ‘yan jarida ba su da masaniya kan manufar KADGESI don haka akwai bukatar kungiyar ta sake dawowa cibiyar Kungiyar domin fadakar da ‘yan Jaridun kan wannan manufa.

“Kuma muna tabbatar muku a matsayinku na Kungiyar cewa da yardar Allah za mu taimaka muku ta hanyar zaburar da mambobinmu don bayar da rahoton shawarwarin da za su kai ga bitar, ba wai don ina nuna son zuciya a matsayina na mace ba, abu ne mai muhimmanci da ya shafe mu kai tsaye.

“Don haka da yardar Allah muna ba da tabbacin 100% na mambobinmu za su tashi tsaye kuma za su taka rawar gani a wannan fanni, ina ganin kafin karshen wannan rana, zan zabi mutum uku da za su shiga cikin tawagar ku.

“Idan a tarihin kungiyarmu a karon farko aka ba ni dama na zo na yi shugabanci, ka ga yana da muhimmanci, don haka me zai hana ku ba sauran matan su ma su ba da gudummawarsu. Ina addu’ar Allah Yasa wanda zai gajena ita ma ta zama mace don mu bar mazan su huta na ɗan lokaci don mu nuna iyawarmu.

“Da yawa daga cikinmu muna jin wannan manufar a karon farko, wasu kadan daga cikinmu sun saba da wannan manufa kuma ina ganin suma sun yi ta rubuce-rubuce a kan wannan manufar, shi ya sa suke yin hakan a nan tare da mu don ba da gudummawarsu.” Ta ce.

Asmau, ta gode wa kungiyar bisa amincewa da kungiyar ta NUJ a matsayin wani bangare na masu ruwa da tsaki da za su ingiza yin nazari tare da aiwatar da manufofin gaba daya.

Tun da farko, wani jami’in kungiyar Rise Up kuma mai gudanar da ayyuka na “Advocacy for Review of KADGESI Policy,” Victor Osae Ihidero, ya shaida wa mahalarta taron cewa bisa lura da kungiyar tasu, manufar KADGESI ba ta samun isasshiyar kulawar kafafen yada labarai, yana mai cewa ba za a iya cimma manufofin Kungiyar ba tare da tallafin kafofin watsa labarai ba.

“Ba za mu iya yin hakan ba tare da ‘yan jarida ba, ba za mu iya cimma burin da muka yi niyyar cimmawa ba tare da ‘yan jarida ba, shi ya sa muka zo nan muka kawo wannan takarda mu bayar da ita a hannun NUJ, domin ku bi ta ku gani ko akwai bangarori na manufofin da za su iya zama wani abu a ciki wanda za ku iya mayar da hankali a kai don rahoto.

“Ba za mu ci gaba da tafiya ba tare da Sakatariyar NUJ a wannan bita ba, domin idan har kafafen yada labarai ba su yi magana a kai ba a yanzu, bayan an gama nazari, gwamnati na iya duba lamarin ta ajiye a gefe idan ana maganar aiwatarwa.

“Amma inda aka samu matsin lamba daga kafafen yada labarai, kuma Gwamna mai zartaswa ya ga ‘yan jarida suna sha’awar hakan, hakan na iya kara masa sha’awar aiwatarwa akoda yaushe, ko mun so ko ba mu so, ina ganin shi ne ya fi kowa sanin jinsi. A Najeriya a halin yanzu gwamnatinsa tana rike da mukaman da aka nada mata kashi 48, abu ne da ya kamata a yi bikin Murnar.

“Kuma idan har ya bar wannan ofishin, ba mu san wanda zai zo ko zai kasance da alaka da jinsi ba, amma idan akwai wata manufa, muna da ka’ida, yana nufin cewa abin da ya samu a cikin lokaci zai iya yin tasiri a ci gaba da zama, wannan ne ya sa muka zo nan domin neman goyon bayan kafafen yada labarai domin bayar da rahotannin shawarwarin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here