Kada Ma’aikata Su Zabi Masu Kuntata Masu – Sakatariyar NLC Kaduna

0
333

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana taron fadakarwa ga ma’aikata da cewa saka ce da aka fara da kyakkyawan zare da nufin kai Najeriya ga tudun muntsira.

Bayanin hakan ya biyo bayan irin taron fadakarwar da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen Jihar Kaduna ta shirya a dakin taro na gidan Kungiyar Malamai dake Kabala kostin Kaduna.

Da take ganawa da manema labarai, Sakatariyar kungiyar, Christiana John Bawa, ta bayyana cewa sun shirya wannan taron fadakarwa ne domin ma’aikata su samu damar tantance duk wani mai son tsayawa takara su tabbatar da ya dace a zabe shi ko bai dace ba.

“Muna son shiga cikin harkokin siyasa musamman ma’aikata su tsaya takarar neman Kujerun yan majalisar Jiha, Tarayya, majalisar Dattawa da Gwamnoni saboda kare mutunci da martabar ma’aika domin idan an samu wani da ke son yin wata dokar da za ta kuntatawa ma’aikata, su ce ba su yarda da dokar ba.”

Christiana, ta ci gaba da bayanin cewa ” akwai wasu Jihohi a Najeriya da har yau ba su iya biyan sabon tsarin albashin ma’aikata ba kuma su na ganin Gwamnonin nasu na fitowa za su yi takarar shugaban kasa duk da halin da Jihohinsu ke ciki, ya dace jama’a fa su du ba idan kana matsayin Gwamna baka ba ma’aikaci hakkinsa ba sai ka zama shugaban kasa ne zaka bashi?

“Kuma idan kana Gwamna ka Kori ma’aikata baka ba su kudin fansho da ko kudin sallama ba sai ka zama shugaban kasa ne zaka bashi? Kai akwai ma wadansu Jihohi da dama da ba su karbi albashin watanni da dama ba saboda haka irin wadannan kowa ya sani idan sun zama shugaban kasa, toh Najeriya za ta mutu”.

Saboda haka muke yin kira ga ma’aikata da su bude idanuwansu kuma su rika jin labarai a rediyo, jaridu da kuma Talbijin domin su San abin da ake ciki.

Saboda haka ina kira ga jama’a da su tabbata duk mai irin wannan in sun tsaya zabe kada su zabe su ko dan majalisa ko wane irin zabe suka tsaya kar su zabe su, koda batun zaben fitar da dan takara ma kada su bari su samu, a zabi wadanda ke da kishin ma’aikata ba irin masu gudun ma’aikata ba akwai kuma wasu da idan an zabe su ba za a kara ganin su ba sai shi kenan don haka irin wadannan mutanen muke yin kira ga ma’aikata da su tabbatar ba su zabe su ba ko kuma su dawo kan kujerunsu”. Inji Christiana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here