Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC Na Kasa Bai Ajiye Aikin Sa Ba

0
381

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

KAMAR yadda muka samu wata takardar da aka rabawa manema labarai da ke dauke da sa hannun babban mai magana da yawun Jam’iyyar APC na kasa Alhaji Salisu Na’inna Dan batta, da aka rabawa manema labarai inda aka tabbatar da cewa Sakataren babban kwamitin rikon na kasa sam bai ajiye mukaminsa ba.

Karin bayani game da taron manema labarai da mai magana da yawun kwamitin rikon APC Barista Ismaeel Ahmed, a bisa hakan ne ake yi wa jama’a bayanin cewa sakataren babban kwamitin rikon shirya zaben APC na kasa Sanata John James Akpanudoedehe, bai aike da takardar ajiye mukaminsa ba jam’iyyar ba.

Bayanin da ke kunshe a cikin takardar ya ce wannan shi ne ainihin abin da yake magana ta gaskiya domin babu wani lokaci da ko aka ce an sallame shi ko sabanin irin yadda wadansu kafafen yada labarai na yanar Gizo ke yada bayanan jita- jita haka kawai ba gaira ba dalili. Don haka duk bayanan karya ne.

Jam’iyyar APC duk abu daya ne ba wani bambanci, don haka kwamitin rikon jam’iyyar wani bangare ne,kuma akwai shugaban kwamitin riko wanda ke ta kokarin ganin an gudanar da babban zaben shugabanni na kasa kuma dukkan yan kwamitin na aiki tukuru ta fuskar goyon baya da kuma ganin an gudanar da zabe Lami lafiya da nufin ganin Najeriya da yan kasar sun ci gaba.

“Saboda haka kada ku amince da duk wadansu bayanai sabanin haka da ake yadawa a kafafen sadarwar yanar Gizo da ba su da tushe balantana makama”.

Leave a Reply