Tsoffin Shugabannin NUJ Kaduna Sun Tabbatar Da Asma’u A Matsayin Sabuwar Shugaba

0
354

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOFFIN shugabannin kungiyar ‘Yan Jaridu ta kasa (NUJ), reshen Jihar Kaduna sun tabbatar da shugabancin Asma’u Yawo Halilu a matsayin sabuwar shugabar cibiyar Kungiyar ta Jihar.

Wannan bayanan ya biyo baya ne kamar yadda tsofaffin shugabannin da suka shedu suka bayyana cewa duk wani abu da ya shafi rikicin zaben shugabancin kungiyar ya kare, sannan kuma sun yi alkawarin marawa shugabancin Asma’u baya.

Tsohon mataimakin shugaban cibiyar Kungiyar, Sabiu Mohammed da sakataren Kungiyar, John Femi Adi ne suka bayyana hakan a yayin taron kungiyar da aka gudanar a ranar Laraba a Kaduna.

Mutanen biyu da suka halarci taron da zummar bada hadin kai, sun kara da cewa kungiyar ta NUJ Kaduna, ta kasance wata babbar iyali ne wanda ‘ya’yanta suke tsintsiya madauri daya, kuma za ta ci gaba da kasancewa a hakan karkashin jagorancin Kwamared Asma’u Yawo Halilu a halin yanzu.

Hakazalika, Kungiyar ta yi nadamar duk wani rikicin da ya biyo bayan bukin kaddamarwar da aka yi wanda ya haifar da sabani a tsakanin wasu ‘ya’yan Kungiyar, kana tana mai baiwa duka al’umma tabbacinta na ganin cewa ta dauki nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na mai sa ido ga al’umma.

“Hakkinmu ne a matsayin wadanda suke matakin kasa ta hudu a mulki domin tabbatar da an yi abubuwan da suka dace na bada sahihan bayanai don ganin an samu daidaito na alhakin da aka dora mana a tsakanin Gwamnati da kuma al’umma domin amfanin kowa da kowa,” Kungiyar ta yanke shawarar.

Da yake magana a madadin sauran shuwagabannin da suka shude, Mista Femi Adi ya bayyana cewa rikicin kungiyar NUJ ta Kaduna ya kare. “Abin da ya faru abu ne na yau da kullum amma, kamar yadda muke magana yanzu, hakan ya kare,” in ji shi.

Kungiyar NUJ ta Kaduna, ta kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna a fannin samar da ababen more rayuwa da ke yaduwa a fadin Jihar, yayin da ta kuma yi kira ga gwamnatin Jihar da ta tashi tsaye wajen magance wasu matsalolin rashin tsaro dake neman addabar wasu yankunan Jihar.

Leave a Reply