Al’ummar Fulani Ku Hada Kai Don Tunkarar Zaben Shekara Ta 2023 – Sarkin Wase

0
365

Daga; Isah Ahmed, Jos.

MAI Martaba Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna, ya yi kira ga al’ummar Fulani na kasar nan, su hada kan su, don tunkarar zabe mai zuwa, na shekara ta 2023. Sarkin ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake jawabi, a wajen bude Sabuwar sakatariyar Kungiyar cigaban al’ummar Fulani ta Najeriya, ta Gan Allah reshen jihar Filato, da aka gudanar a garin Jos.

Ya ce al’ummar Fulani suna da mutum a kalla miliyan 12 a Najeriya, wadanda suka cancanci jefa kuri’a. Don haka idan suka hada kai, zasu iya zaben wanda suke so ya shugabance su a Najeriya.

Sarkin wanda Galadan Wase Alhaji Mustapha Umar ya wakilta, ya yi kira ga Fulanin su mayar da hankali wajen ilmintar da ‘yayansu tare da koya masu sana’o’i, domin su taimaki kan su da al’umma baki daya.

” Ya zama wajibi al’ummar Fulani su duba irin halin da suka tsinci kansu a ciki. Muna son daukacin Fulani su yi gangamin wayar da kan matasa, domin a zauna lafiya da juna domin a samu ci gaba, domin idan babu zaman lafiya, babu wata gwamnati da za ta fara gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su amfanar da jama’a .”

Shima a nasa jawabin, Shugaban riko na Kumgiyar ta Gan Allah na Kasa, Alhaji Sulaiman Yakubu ya yi kira ga al’ummar Fulani su sanya yayansu a makaranta, domin ilmi ne gishirin zaman duniya.

Ya ce babu abin da zai ceto al’ummar Fulan,i daga mawuyacin halin da sule ciki, kamar ilmi.

Har’ila yau ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni, su ba su goyon baya wajen gyara makarantun makiyaya na kasar nan.

A nasa jawabin Sakataren kungiyar na kasa Alhaji Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa kungiyar, ta yanke shawarar sanya sunan tsohon Shugaban kungiyar na Kasa, Marigayi Alhaji Sale Bayari, a sabuwar Sakatariyar kungiyar da za a bude a Abuja, da kuma dukkan ofisoshinta na Jihohin.

Ya ce kungiyar ta yanke wannan shawara ce, domin tunawa da irin guduawar da marigayin ya yi, wajen kafuwar kungiyar da kuma taimakawa al’ummar Fulanin Najeriya baki daya, a lokacin da yake raye.

Sakataren ya yi bayanin cewa daga lokacin da aka kafa wannan kungiya, zuwa yanzu an sami nasarar kafa kwamitin malamai da yake bin rigagen Fulani yana yi masu wa’azi da wayar masu da kai.

“Mun bude makarantu guda 6 da asibitocin mutane da dabbobi da wuraren koyar da ilmin kwanfuta da koyan sana’o’i a rigagen Fulani”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here