Kungiyar ci gaban al’ummar Jere za ta  gina cibiyar koyar da sana’o’i a garin  Jingir

0
339


Daga Isah Ahmed, Jos
Shugaban Kungiyar cigaban al’ummar Kabilar  Jere ta Kasa [JENDA], da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato,  Rebaran  Samuel Baqo Mamman, ya bayyana cewa Kungiyar zata gina, wata katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i daban daban, da zasu kashe kudi sama da Naira miliyan 15, a garin Jingir da ke Karamar Hukumar Bassa, a Jihar Filato. Shugaban qungiyar ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar Kabilar Jere, da aka gudanar a garin Jingir, a karshen makon da ya gabata.
Ya ce zasu gina wannan cibiya ta  koyar da matasa da sana’o’i daban daban ne,  domin su tallafawa matasan wajen ganin sun dogara da kansu.
Ya ce tuni sun riga sun sami fili a garin Jingir, da zasu gina wannan cibiya, wadda suke  sa ran  kashe kudi  Naira miliyan 15, wajen aikin gina cibiyar.
Ya yi  kira ga al’ummar Jere, su zo su hada kai  su tallafawa matasansu su tafi makaranta da koya masu  sana’o’i domin su dogara da kansu, su tallafawa wasu.
Shima a nasa jawabin, Shugaban Hukumar kididdiga ta Kasa Dokta Semon Harry ya bayyana cewa, babu shakka aikin gina wajen koyon sana’a da wannan kungiya zata yi, yana da mutukar mahimmanci.
Ya ce matasanmu da suka gama makaranta, zasu iya zuwa su koyi sana’o’in da zasu iya rike kansa batare da tsayawa suna neman aikin gwamnati ba, a wannan cibiya.
Ya yi   kira ga al’umma kan a  tallafawa wannan aiki, na gina wajen koyon sana’a da wannan jungiya ta kuduri aniyar yi.
 Ya yi  kira ga kungiyoyin raya yankin  Pengana, su cigaba da wayar da kan matasa, kan mahimmancin zaman lafiya, domin sai da zaman lafiya ne za a iya yin komai na cigaba.
A nasa jawabin Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, a majalisar Dattijai Sanata I.V. Gyang ya yabawa al’ummar yankin Pengana, kan zaman lafiyar da suke yi.
Ya yi  kira ga iyaye su kara himma wajen ilmintar da ‘yayansu, domin ta  haka ne,  za a sami cigaba.
Shima a nasa jawabin, Mai martaba Ujah Anaguta Samuel Jauro Magaji, ya yi kira ga al’ummar Jere,  su cigaba da yiwa kasar nan addu’a, domin Allah ya warware mana halin da muke ciki na rashin zaman lafiya.
Shi dai wannan taron ranar ta Kabilar Jere, ya sami halartar ‘yan kabilar da sauran jama’a daga wurare daban daban, na kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here