Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeAddiniFarfesa Mansur Yelwa...

Farfesa Mansur Yelwa ya sauka daga limancin masallacin jami’ar ATBU

Tsohon babban limamin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, Farfesa Mansur Isa Yelwa, ya bayyana cewa amincewar da mahukuntan jami’ar suka bai wa ƙungiyar ɗaliban Tijjaniyya (TIMSAN) domin gina masallaci a harabar jami’ar ce ta sa ya yi murabus daga mukaminsa.

Farfesa Yelwa ya ce amincewa da gina masallacin na iya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ɗalibai da mabiya ƙungiyoyi daban-daban a jami’ar.

Ya bayyana cewa idan aka bai wa Tijjaniyya damar gina masallaci, sauran ƙungiyoyi irin su Ƙadiriyya, Izala, Salafiyya da Shi’a ma za su nemi irin wannan dama, lamarin da ka iya kawo rashin jituwa a jami’ar.

Ku kuma karanta: A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa

Tsohon limamin ya ce tun lokacin da ya zama babban limami shekaru 17 da suka gabata, ya yi aiki wajen haɗa kan musulman jami’ar ba tare da nuna bambanci ba, amma ya yi zargin cewa an ba da wannan izini ba tare da tuntubar sa ba.

Ya bayyana cewa ba zai koma mukaminsa ba har sai mahukuntan jami’ar sun janye amincewar da suka bai wa TIMSAN.

Sai dai daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Zailani Bappa, ya kare matakin da jami’ar ta ɗauka, yana mai cewa an bi doka da ƙa’ida wajen bayar da izinin.

Ya ce jami’ar ba za ta hana duk wani halastaccen aikin addini da ba ya barazana ga zaman lafiya ba, yana mai ƙara da cewa ƙungiyar TIMSAN ba ta nemi gina sabon masallacin Juma’a ba, sai dai filin gudanar da wasu ayyukanta na addini.

Bappa ya kuma bayyana cewa majalisar SHURA ta musulman jami’ar ta shiga cikin tattaunawar da aka yi kafin a amince da buƙatar, yana mai jaddada cewa jami’ar na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai da mazhabobi daban-daban.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Allah Ya yiwa fitaccen ɗan wasan Barkwanci, Sani Tumbeleƙe rasuwa

Allah Ya yiwa fitaccen ɗan wasan Barkwanci, Sani Tumbeleƙe rasuwa Rahotanni daga Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna, ya bayyana cewa fitaccen wasan Barkwanci nan Sani Gwarzo Tumbeleƙe rasuwa. Ku kuma karanta: ‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta...

‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a da sakamako mafi daraja

'Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari'a da sakamako mafi daraja Wata matashiya mai shekaru 24, Aisha Widad Yahaya, wadda ita ce uwa ga yaro ɗaya kuma matar aure, ta kafa...

An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

An yi jana'izar 'yan Shi'a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba'een a Abuja 'Yan'uwa Musulmi, Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da jana'izar 'yan'uwa biyar a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ranar Laraba,...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.