Ya Kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci Ya Zurfafa Tunani da Ƙwarewa Wajen Haɓaka Harkokin Isar da Saƙo — Dr. Hassan Gimba
Taron Makon Yaɗa Labaran Harkar Musulunci, wanda ke gudana da taken “Ƙarfafa Ƙwarewar Yaɗa Labarai Domin Isar da Saƙon Harkar Musulunci Cikin Inganci”, ya shiga rana ta biyu a yau Asabar, 11 ga Jimada Sani, 1448H, daidai da 21 ga Nuwamba, 2026, a birnin Abuja.
Bayan kammala sallah da cin abinci, an ci gaba da gudanar da zaman taron, inda aka gabatar da Dr. Hassan Gimba mamallakin jaridar Neptune Prime, wanda ya gabatar da maƙala mai taken: “Tasirin Gidajen Jaridu Wajen Sauya Tunanin Al’umma”.
Ku kuma karanta: Fatima Barnawi Bafalasdiniya Yar Gwagwarmaya Yar Asalin Najeriya
A farkon jawabinsa, Dr. Gimba ya bayyana yadda suka sha gwagwarmaya a farkon-farkon da’awa wajen isar da saƙonni, duk da ƙalubale da barazanar rasa rayuwa da suka fuskanta.
Ya ci gaba da bayanin yadda aka yi amfani da jaridu wajen sauya tunanin al’umma da fahimtar kiran da Jagora Shaikh Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H) yake yi.


“A farkon-farkon gwagwarmaya, an yi amfani da jaridu wajen sauya tunanin al’umma kan hadafin Da’awar Harkar Musulunci,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, bai kamata ’yan’uwa su bari mutanen gari ne kawai suke bayyana wa duniya ko su waye ba. A maimakon haka, ya kamata su kasance masu amfani da dukkan hanyoyin yaɗa labarai wajen isar da saƙonninsu ga al’umma.
Da yake magana kan muhimmancin rashin nuna wariya a aikin jarida, Dr. Gimba ya ce:
“Matsayinka na mai ba da labari, ko da kana saɓani da wani ne, ya wajaba ka faɗi gaskiya a kansa. Duk wani saƙon da kake son isarwa, ka tabbatar da cewa gaskiya ce kake bayyanawa.”
Dr. Hassan Gimba ya ba mahalarta damar yin tambayoyi, inda suka gabatar da tambayoyinsu, kuma ya amsa su nan take. Ya kuma shawarci ’yan Dandalin Yaɗa Labarai da su ƙara jajircewa wajen yin gogayya da sauran ’yan jaridu a ƙasa.
A cikin shawarwarinsa, ya jaddada cewa:
“Ya kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci ya zurfafa tunani da ƙwarewa wajen haɓaka harkokin isar da saƙon Harkar Musulunci.”
Haka kuma, a cikin jawabinsa, Dr. Gimba ya bayyana yadda aka kafa jaridar Pointer Express ta Harkar Musulunci, tare da irin gwagwarmayar da aka sha wajen yi wa jaridar rajista.
Bayan kammala jawabin Dr. Hassan Gimba, sai aka gabatar da Malam Saminu Sani, daga Liberty TV da Rediyo, inda ya gabatar da maƙalarsa mai taken: “Kafafen Yaɗa Labarai: Talabijin da Rediyo, Gudummawarsu da Muhimmancinsu Wajen Isar da Saƙo”.
A cikin jawabinsa, Malam Saminu Sani ya yi cikakken bayani kan irin gudunmawar da talabijin da gidajen rediyo suke takawa wajen isar da saƙonni ga al’umma, tare da bayyana muhimmancinsu a harkokin sadarwa. Har wala yau ya yi dogon bayani kan tarihin kafuwar rediyo da talabijin.
“Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙo,” in ji shi.


