Iran na shirin kai mana harin bam a birnin Washington – Amurka
Hukumomin leken asirin Amurka sun gano bayanan da ke nuna cewa Iran na shirin yiwuwar kai hari kan wasu manyan jami’an gwamnatin Shugaba Donald Trump a birnin Washington, ta hanyar amfani da bam mai gurbata muhalli ko makamin sinadarai.
Rahoton da jaridar Tribune Online ta wallafa, bisa bayanan jami’an Amurka bakwai, ya ce hukumomin sun gano wasu wurare da ake zargin za su iya zama wuraren kai harin, lamarin da ya sa Amurka ta fara shirye-shiryen kare kanta.
Sai dai mai magana da yawun Fadar White House, Lauren Bis, ta ce gwamnatin na sanya ido kan duk wata barazana, amma babu wata sahihiyar barazanar kai hari cikin kasar a halin yanzu.
Ku kuma karanta: Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam’iyyarmu rashin nasara – Trump
Bayanan leken asirin sun kuma nuna yiwuwar Iran ta riga ta tanadi wasu kayayyakin hada bama-bamai ko sinadarai a cikin Amurka, duk da cewa jami’ai na da sabanin ra’ayi kan sahihancin bayanan.
Bam mai gurbata muhalli na amfani da abubuwa masu hasken rediyo tare da abubuwan fashewa domin yada gurbatar sinadarai masu illa ga lafiyar al’umma. Ba ya da karfin fashewar makamin nukiliya, amma yana iya haddasa cututtuka da sanya wasu yankuna zama marasa aminci.
A nata martanin, Iran ta musanta zargin shirin amfani da makaman sinadarai, tana mai cewa amfani da irin wadannan makamai ba shi da halacci a kowane yanayi.
Rahoton ya ce ana ci gaba da samun zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu sakamakon hare-haren sojin Amurka kan Iran da kuma takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba mata.


