Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

OECD 2024 raporuna göre, Avrupa’daki lisanssız bahis sitelerinin oranı %35’tir; bu, bettilt giriş gibi lisanslı sitelerin önemini artırır.

bahsegel bahsegel giriş bahsegel bettilt bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş paribahis

Dijital ortamda oyun keyfini artıran https://paribahis-resmi.ink/ kategorileri öne çıkıyor.

bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bettilt bettilt güncel giriş
HomeLabariHisbah ta kama...

Hisbah ta kama ‘yan TikTok mata 17 a Kano

Hisbah ta kama ‘yan TikTok mata 17 a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu mata matasa 17 bisa zargin yin rawa a kafar sada zumunta ta TikTok da kuma wasu da ake zargin suna yawo a wuraren da ba su dace ba a cikin birnin Kano.

An kama matan ne a wurare daban-daban, ciki har da wasu otel-otel, bisa zargin aikata abubuwan da hukumar ke ganin sun saba wa ƙa’idojin ɗabi’a.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Malam Mujahideen Aminuddeen, ne ya tabbatar da kamen ga jaridar Daily Trust a Kano.

Ya ce kamen wani ɓangare ne na samamen da hukumar ke ci gaba da gudanarwa domin dakile ayyukan da suka saɓa wa dokokinta da ƙa’idojin tarbiyya.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta kama wasu masu tuka babura masu kafa uku (Adaidaita Sahu) bisa zargin ɗaukar mata fasinja a gefen da direba yake zaune.

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne a wurare daban-daban na jihar yayin sintiri da ayyukan sa ido da hukumar ke gudanarwa.

Mujahideen ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama ba su da cikakken ilimin addinin Musulunci, inda wasu ma ba sa iya karatu ko gudanar da ibadun yau da kullum yadda ya kamata.

Ya ce saboda haka hukumar ta fara shirye-shiryen koyar da su yadda ake alwala da sallah da sauran muhimman abubuwan addinin Musulunci.

“Mun gano cewa wasu daga cikinsu ba su da ilimin addini na asali. Muna shirye-shiryen koya musu alwala, sallah da sauran abubuwan da suka shafi ilimin Musulunci,” in ji shi.

Mataimakin kwamandan ya ƙara da cewa waɗanda aka kama za su ci gaba da kasancewa a hannun hukumar na wani lokaci domin samun karatun addini.

Ya ce manufar matakin ba hukunta su kaɗai ba ce, illa gyara halayensu da cusa musu kyawawan ɗabi’u.

Haka kuma, jami’in Hisbah ɗin ya jaddada aniyar hukumar na ci gaba da gudanar da aikinta na tabbatar da ɗa’a da yaƙi da munanan ɗabi’u a faɗin jihar.

Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su ƙara sanya ido kan harkokin ‘ya’yansu, musamman yadda suke amfani da kafafen sada zumunta da kuma mu’amalarsu a wuraren taruwar jama’a.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

An Sace Sola Fanel 25 a Saman Masallacin Kanzul Mudalsam da ke Kano

An Sace Sola Fanel 25 a Saman Masallacin Kanzul Mudalsam da ke Kano Wasu da ake zargin barayi ne sun saci fanal guda 25 a saman masallacin Kanzul Mudalsam da ke unguwar Gwammaja, a kan titin hanyar Katsina a birnin...

Jikan Sheikh Nasir Kabara, Almaliky ya zo na ɗaya a gasar waƙoƙin yabon Annabi (S) a Kano

Jikan Sheikh Nasir Kabara, Almaliky ya zo na ɗaya a gasar waƙoƙin yabon Annabi a Kano Mawaƙi Nasir Almaliky, jikan fitaccen Malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Nasiru Kabara ya zo na farko a gasar waƙoƙin yabon Annabi Muhammad (SAW) da...

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara kaimi wajen ganin an kammala manyan ayyukan layukan dogo da ake gudanarwa a Arewacin Najeriya, inda...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.