2027: Ku karɓi kuɗin kamfen, amma ku zaɓi wanda ku ke so – Makinde
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Gwamna Seyi Makinde, ya shawarci ’yan Najeriya da su karɓi kuɗin da ’yan siyasa ke ba su yayin kamfen, amma su zaɓi wanda suka ga ya dace da lamirinsu.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kamfen ɗinsa na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a jihar Bauchi.
Ya ce bai kamata karɓar kuɗin siyasa ya zama dalilin zaɓen ɗan takarar da masu zaɓe ba sa so ba.
Ku kuma karanta: Obi ya bukaci Tinubu ya dakatar da shirin kafa ‘yasandan jihohi sai bayan zaɓen 2027
A kalamansa, “Idan suka kawo kuɗi, kuɗin ku ne. Ku karɓa, ku kashe, amma ku zaɓi wanda zuciyarku take so.”
Dan takarar ya kuma yi kira da a yi wa Najeriya garambawul, yana mai cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da ware wasu ’yan ƙasa daga harkokin mulki sun nuna bukatar sauyi a tsarin tafiyar da ƙasar.
Ya ce yunwa da matsalolin tsaro da ake fuskanta na buƙatar sake duba manufofin tattalin arziki da tsarin tsaron ƙasar domin samar da gwamnati mai gaskiya da adalci.


