Tinubu ga Atiku: Rashin iya shugabancin ka ne ya sa ka rusa PDP, ka gudu ka bar ta
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da rashin ƙwarewar jagoranci, yana mai cewa ya bar jam’iyyar PDP ne lokacin da aka fara nuna alamun ƙalubalantar shugabancinsa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani liyafar cin abinci da gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shirya masa.
Shugaban ya ce Atiku ya gudu daga PDP lokacin da wasu mambobin jam’iyyar suka fara shirin ƙalubalantar matsayinsa, inda ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin neman takarar shugabancin ƙasa.
Ya tambayi ‘yan Najeriya ko za su amince su ba mutumin da ya kasa ɗaukar nauyin jagoranci a matakin jam’iyya amanar shugabancin ƙasa.
Ku kuma karanta: Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam’iyyarmu rashin nasara – Trump
Tinubu ya kuma yi ikirarin cewa kafin ya hau mulki, gwamnonin jihohi 27 daga cikin 36 ba sa iya biyan albashi, fansho da alawus-alawus, amma ya ce gwamnatinsa ta shawo kan matsalar.
Haka kuma, ya sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da aikin tashar jiragen ruwa ta Akwa Ibom Deep Seaport, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta cika nata alƙawarin.
Tinubu ya bayyana zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027, a matsayin zaɓe mai muhimmanci da zai fayyace makomar Najeriya.
Atiku dai ya taɓa barin PDP a shekarun 2006 da 2014, kafin ya sake ficewa daga jam’iyyar a ranar 14 ga Yuli, 2025.


