Me ya yi sanadiyar mutuwar Likitoci Biyu Tagwaye A Yobe ?
Dakta Hadiya Usman da Dakta Aidah Usman, ’yan tagwaye mata kuma ’ya’yan Babban Daraktan Kiwon Lafiya (CMD) na Federal Medical Centre (FMC), Nguru, Jihar Yobe, sun rasu cikin tazarar kwanaki biyu kacal a tsakani.
A wani lamari mai matuƙar taɓa zuciya, ’yan’uwa tagwayen juna, ɗaya cikakkiyar likitar asibiti (Medical Doctor), ɗayar kuma likitar magunguna mai digirin Doctor of Pharmacy (PharmD), sun rasu cikin kwanaki biyu kacal a tsakani, lamarin da ya jefa iyalansu, abokan aikinsu da kuma al’ummar ma’aikatan lafiya cikin babban alhini da jimami.
Dakta Hadiya Usman, wadda aka fi sani da Hassana, cikakkiyar likitar asibiti ce, kuma ta rasu ranar Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya. ’Yar uwarta, Dakta Aidah Usman, wadda aka fi sani da Hussaina, kuma likitar magunguna ce, ta rasu ranar Lahadi, kimanin sa’o’i 48 kacal bayan rasuwar ’yar’uwarta.
Ku Kuma Karanta: Kotu a Kano ta Aike Wa Da Malam Lawan Triumph Sammaci kan Zargin Wa’azin Tunzura Jama’a
A cewar majiyoyin ‘yan’uwan, ’yan’uwan biyu sun kasance suna fama da cutar sickle cell.
Abin da ya faru da Dakta Aidah ya ƙara sanya wannan rashi zama mai matuƙar raɗaɗi. Bayan kwana biyu da binne ’yar tagwarta Hadiya, an ce Dakta Aidah ta je maƙabarta da aka binne ’yar’uwarta. A lokacin da take a wajen kabarin, sai kawai ta faɗi sumammiya. Nan take aka garzaya da ita asibiti domin a ba ta kulawar gaggawa.
Sai dai bayan shafe wasu sa’o’i a asibiti ana ƙoƙarin ceto rayuwarta, Allah Ya karɓi ranta.
Marigayan ’yan tagwayen biyu ’ya’ya ne ga Dakta Hadiza Usman, shugabar Asibitin Federal Medical Centre (FMC), Medical Director (MD) Nguru, Jihar Yobe.

Da suke tabbatar da faruwar lamarin, ‘yan’uwan tagwayen sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi mai ɗaci da ya girgiza iyalan da kuma al’ummar ma’aikatan lafiya baki ɗaya.
Al’umma suna ta alhini da jimamin wannan rashi. Wasu suka ce,
«“Sun zo duniya tare, kuma sun koma ga Allah tare.”»
«“Lallai Allah ne Mafi Tsarin al’amura.”»
Labarin rasuwar ’yan tagwayen ya jefa mutane cikin jimami sosai, musamman a shafukan sada zumunta, inda abokan aiki, abokai da ’yan uwa da sauran masu fatan alheri suka bayyana matuƙar kaɗuwa, baƙin ciki da jajantawa iyalan marigayin.
’Yan’uwan tagwayen biyu sun bar wannan duniya cikin tazarar kwanaki kaɗan—ɗaya ranar Juma’a, ɗayar kuma ranar Lahadi.
Haƙiƙa, ƙaddarar Allah ta fi ƙarfin fahimtar ɗan Adam. Allah Ya jiƙan su, Ya gafarta musu, Ya sa Aljanna ce makomarsu, Ya kuma ba iyalansu da ’yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.


