Alaƙa tsakanin Isra’ila da Qatar na ƙara tsami: Isra’ila ta haramta fitar da kayayyakin masana’antun sojinta zuwa Qatar
Rahotanni daga Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin hana fitar da duk wani samfurin da ya shafi masana’antun sojojinta zuwa Qatar, a wani sabon mataki da zai iya ƙara tsananta dangantaka tsakanin bangarorin.
A cewar Tashar Channel 13 ta Isra’ila, an yanke shawarar dakatar da duk wani nau’in fitar da kayayyakin da ke da alaƙa da masana’antun tsaro da na soji na Isra’ila zuwa Qatar.
Rahoton bai bayyana cikakken jerin kayayyakin da wannan takunkumi ya shafa ba, amma matakin ya shafi kayayyakin da ake ƙera wa ko kuma suke da alaƙa da masana’antun sojin Isra’ila.
Ku kuma karanta: Amurka ta bayyana mutane 5 da suka kai hare-hare ta intanet a kan muhimman cibiyoyin ta
Ana kallon wannan mataki a matsayin wani sabon sauyi a manufofin Isra’ila game da Qatar, wadda a shekarun baya ta taka rawa wajen shiga tsakani kan wasu batutuwa masu alaƙa da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Masu sharhi kan harkokin siyasa da tsaro na ganin cewa irin wannan mataki na iya ƙara nuna tsamin dangantaka tsakanin Tel Aviv da Doha, musamman a lokacin da ake ci gaba da samun rikice-rikice da takaddama kan batutuwan tsaro a yankin.
Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan dalilin da ya sa Isra’ila ta ɗauki wannan mataki ba, ko kuma ko Qatar za ta mayar da martani da wani mataki makamancin haka.
Ana ci gaba da jiran ƙarin bayani daga hukumomin Isra’ila da Qatar kan sabon matakin da kuma irin tasirin da zai iya haifarwa ga dangantakar ƙasashen biyu.


