HomeJami'aLakcaran da aka...

Lakcaran da aka lakaɗa wa duka kan zargin lalata da ɗaliba, ba ma’aikacin mu ba ne – MAAUN

Jami’ar Maryam Abacha American University Kano, ta fitar da sanarwar cewa Dr. Nasa’i Gwadabe, Lakcaran da aka lakaɗa wa duka kan zargin lalata da ɗaliba, ba ma’aikacin ta ba ne, sai dai ya yi aiki ne a jami’ar a matsayin ʼvisiting lecturerʼ na tsawon shekara guda, amma wa’adin aikinsa ya ƙare a watan Mayun 2026, kuma ba a sabinta kwantiraginsa ba. Kamar yadda Malam Ali Kakaki na Jami’ar MAAUN ɗin ya sanar.

Ku kuma karanta: Farfesa Mansur Yelwa ya sauka daga limancin masallacin jami’ar ATBU

Kazalika jami’ar ta musanta rahotannin da ke cewa wata ɗaliba ta shafe shekara biyu ba tare da kammala karatu ba, da kuma zargin cewa akwai ɗalibar da ke digiri na biyu da abin ya shafa.

MAAUN ta jaddada cewa tana da manufar hana cin zarafi ta hanyar lalata, tare da buƙatar kafafen yaɗa labarai da jama’a su riƙa bayar da rahotanni bisa sahihan bayanai.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Kotu ta umarci Sheikh Abduljabbar ya gabatar da litattafan da ya yi amfani da su wajen kafa hujja a shari’ar farko

Babbar kotun jihar Kano mai sauraron ƙorafe-ƙorafen ɗaukaka ƙara ta saurari ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar yana ƙalubalantar hukuncin kisa da Kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu ta yanke masa kan zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad...

Farfesa Mansur Yelwa ya sauka daga limancin masallacin jami’ar ATBU

Tsohon babban limamin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, Farfesa Mansur Isa Yelwa, ya bayyana cewa amincewar da mahukuntan jami’ar suka bai wa ƙungiyar ɗaliban Tijjaniyya (TIMSAN) domin gina masallaci a harabar jami’ar ce ta sa ya...

A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa

Matashi a garin Gashuwa ta jihar Yobe, mai suna Umar Aminu Ahmad, wanda aka fi sani da Umar Ɗan Paleti, ya ɗauki buhun shinkafa a kansa, mai nauyin kilogram 100 inda ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, don ya...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.