Ƙungiyar Manoma Ta Ƙaddamar Da Dalar Masara A Kaduna

0
656

Daga; Rabo Haladu, Kaduna.

ƘUNGIYAR manoma ta kaddamar da dalar buhunan masara a jihar Kaduna, a wani yunƙuri da hukumomi ke cewa na nuna irin ci gaban da aka samu a ƙasar ta fuskar noman masarar.

SHIRIN dalar masara tsari ne na hadin-gwiwa tsakanin ƙungiyar manoman masara da Babban bankin Najeriya wato CBN, karkashin shirin bada tallafi ga manoma na Anchor Borrower Programme.

Ana saran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar wadanda suka samu tallafin Anchor Borrower Programme.

Wannan na zuwa ne sama da mako biyu bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar, in ji gwamnatinsa.

Shugaban kungiyar manoman masara ta Najeriya, Alhaji Bello Abubakar Funtuwa ya shaida cewa an tara dalar masara ce don bayyana wa duniya irin nasarorin da aka samu a noman masara a ƙasar.

Ya ce “rancen da ake bai wa manoma ya taka rawa wajen bai wa manoma damar tara irin wannan masara, kuma wannan somin-taɓi ne.”

“Duk da cewa suna fuskantar matsalolin tsaro a kauyuka, hakan bai hanasu tara masara ba. Amma muna fatan tsaro ya inganta, saboda noman ya fi wanda aka gani a yanzu.”

Shirin na gwamnatin na zuwa ne adaidai lokacin da ‘yan kasa ke kokawa da yadda kayan abinci ke tashin gauron-zabi, inda a yanzu haka buhun masarar na kai wa dubu 22.

Wannan dalilin ne ya sanya wakilinmu yaji daga bakin mahukunta kan ko kaddamar da wannan dala za ta sauya farashi ko akwai wani sauyi da za a gani.

Mal Ibrahim Husseini, shi ne kwamishinan Noma da ya wakilci gwamnan Kaduna a wajen kaddamar da dalar masarar, wanda ya shaida mana cewa kasuwa ce ke tabbatar da farashi.

Kwamishinan ya ce abu muhimmin a yanzu shi ne kokarin tabbatar da wadatuwar abinci a kasar.

“Wannan tsari tabbas farashi ya sauka da lokaci, kuma manoma ke sayar da kayansu ba za a kayyade musu ba, ya danganta amma suna kan tsrai.”

Ana saran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa tana daukan matakan bunkasa harkar noma domin rage abinci da ake shigar da su kasar daga ketare.

Shugaba Buhari a lokacin kaddamar da irin wannan dala amma ta shinkafa a watan Janairu ya ce ana samun irin wannan nasara ne sakamako juye-juyen halin da gwamnatinsa ta ƙaddamar ta fuskar noma domin tabbatar da cewa ƴan Najeriya na iya noma abin da za su ci kuma su ci abin suka noma.

Gwamnati dai ta ce kawo yanzu shirin Anchor Borrowers ya tallafa wa ƙananan manoma miliyan 4.8; wajen noma nau’ukan amfanin gona har iri 23 da suka haɗa da shinkafa, da masara da kwakwar manja, da koko, da auduga, da rogo da tumatur da kuma wajen kiwon dabbobi.

Leave a Reply